Boko Haram: Sojoji sun kafa dokar hana fita a Maiduguri

Rundunar Sojin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Maiduguri fadar Jihar Borno sakamakon yunkurin kai hare-haren da ’yan Boko Haram suka yi a shekaranjiya Laraba. Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari a kusa da birnin Maiduguri a yammacin Larabar.Kakakin Rundunar Sojin […]

Boko Haram: Sojoji sun kafa dokar hana fita a Maiduguri
Boko Haram: Sojoji sun kafa dokar hana fita a Maiduguri

Rundunar Sojin Najeriya ta sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Maiduguri fadar Jihar Borno sakamakon yunkurin kai hare-haren da ’yan Boko Haram suka yi a shekaranjiya Laraba.

Rahotanni sun ce wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan Boko Haram ne sun kai hari a kusa da birnin Maiduguri a yammacin Larabar.
Kakakin Rundunar Sojin Najeriya, Kana Sani Usman Kuka-Sheka, ya shaida wa BBC cewa an sanya dokar hana fitar ne domin fatattakar maharan da suke neman kaddamar da hare hare a birnin Maiduguri.
Kanar Kuka-Sheka ya ce sojoji sun dakile yunkurin kai harin na yammacin Laraba. Kuma ya bukaci mazauna birnin Maiduguri su mutunta dokar hana fitar, sannan su taimaka wa jami’an tsaro ta yadda za a samu nasarar murkushe ’yan Boko Haram din.
Wasu mazauna birnin sun ce koda yake dokar za ta takura wa jama’a, amma tana da muhimmanci domin kare rayukansu.
Harin na shekaranjiya ya zo ne a daidai lokacin hukumomin bada agaji na duniya suka fara kokawa cewa ’yan gudun hijirar Boko Haram da daukacin al’ummar Lardin Arewa mai nisa a Kamaru na fuskantar matsalar karancin abinci.
Sun yi kira ga kasashen duniya su taimaka don ba jama’ar yankin da bakinsu damar ci gaba da rayuwa.
Babban Jami’in Hukumar Kula da Bayar da Abinci ta Majalisar dinkin Duniya reshen Kamaru, Jack Roy, ya ce kashi 19 cikin 100 na yaran da ke yankin na fama da tamowa.
Mista Roy ya ce “Muna bukatar Dala miliyan 30 domin samar da abinci ga daukacin ’yan gudun hijirar wannan yanki.”