Boko Haram sun fille kan masunta 14 a kan iyakar Najeriya 

An kai musu harin ne yayin da suke kamun kifi a kusa da Bosso a ranar Lahadi. 

Boko Haram sun fille kan masunta 14 a kan iyakar Najeriya 

’Yan ta’addan Boko Haram, sun yi wa masu kamun kifi 14 kisan gilla, a yankin Diffa da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Masu kamun kifin sun bar Arewa Maso Gabashin Najeriya domin guje wa hare-haren Boko Haram.

An kai musu harin ne yayin da suke kamun kifi a kusa da Bosso a ranar Lahadi.

Shugaban ƙungiyar ’yan sa-kai da ke taimaka wa sojojin Najeriya, Babakura Kolo, ya ce ’yan ta’addan sun sare wuyan masu kamun kifin su 14.

Mutanen da aka kashe sun fito daga yankin Malam Fatori da Doron Baga na Najeriya.

Sun gudu zuwa Nijar ne saboda rikicin Boko Haram da ke ci gaba da tsamari a Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Yankin Diffa, wanda ke kan iyaka da Najeriya da Chadi, ya sha fama da hare-haren Boko Haram da kuma ƙungiyar ta’addanci ta mai suna ISWAP.

Duk da ƙoƙarin sojoji, yankin na ci gaba da zama cikin hatsari.

Ɗaya daga cikin ’yan sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), Ibrahim Liman, ya tabbatar da harin da adadin mutanen da aka kashe.

Tsawon shekara 15, Arewa Maso Gabashin Najeriya na fama da hare-haren Boko Haram, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 400,000 tare da raba kusan mutum miliyan biyu da muhallansu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kusan ’yan Najeriya 138,000 ne suka gudu zuwa Nijar don neman mafaka.

Yawancin waɗanda rikicin ya raba da muhallansu sun dogara da kamun kifi ne da wasu ƙananan sana’o’i don yin rayuwa, amma ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya sun hana su zaman lafiya.

Ƙungiyoyin suna zargin su da taimaka wa sojoji ko ƙungiyoyin sa-kai.

A watan Mayu, mayaƙan ISWAP sun kashe ɗaruruwan masu kamun kifi a tsibirai da ke Tafkin Chadi, idan suka ayyana harin a matsayin fansa ga farmakin da sojoji suka kai wanda ya yi sanadin lalata sansaninsu.

Tafkin Chadi, wanda ya haɗa Najeriya, Nijar, Kamaru, da Chadi, ya kasance mafakar Boko Haram da ISWAP, inda suke amfani da shi wajen kai wa ƙasheshe hare-hare.