Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da ofishin ’yan sanda
Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi ƙoƙarin ƙwace sansanin sojoji da ke yankin.
Wasu mayakan Boko Haram
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Logomani da ke Ƙaramar Hukumar Ngala a Jihar Borno, inda suka ƙone wani ofishin ’yan sanda da cibiyar kula da lafiya.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma yi ƙoƙarin ƙwace sansanin sojoji da ke yankin.
- Gwamnati ta ƙara albashin sojoji — Ministan Tsaro
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 a wani sabon hari a Filato
Mukaddashin Jami’in Yaɗa Labarai na Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammed Goni, ya ce sojoji sun daƙile harin tare da fatattakar maharan.
Sai dai ya ce soja guda ya rasu, yayin da motocin yaƙi guda biyu da wasu kayan aikin rundunar suka lalace.
Ya ce, maharan sun samu shiga wani ɓangare na sansanin yayin artabu, amma sojojin sun sake tsara kansu tare da mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa bayan sun yi asara.
Goni ya kuma ce sojojin Bataliya ta 115 sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Askira/Uba, tare da ƙwato Naira miliyan 1.2 da kayan abinci da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen tallafa wa ayyukan ’yan ta’adda.