Boko Haram sun kashe manoma 4 da kona gawarsu a Borno

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kaiwa gonakin shinkafar unguwannin Zabarmari da Koshebe a yammacin ranar Asabar yayin da suka kashe manoma 4 da kuma kona gawarwakinsu. Unguwannin sun kai nisan kilomita 10 zuwa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno. Wadanda ake zargin a ranar 1 da Disamba sun kai hari gonakin […]

Boko Haram sun kashe manoma 4 da kona gawarsu a Borno

Mayakan Boko Haram

Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kaiwa gonakin shinkafar unguwannin Zabarmari da Koshebe a yammacin ranar Asabar yayin da suka kashe manoma 4 da kuma kona gawarwakinsu.

Unguwannin sun kai nisan kilomita 10 zuwa garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Wadanda ake zargin a ranar 1 da Disamba sun kai hari gonakin shinkafa inda suka lalata hekta-hekta na gonakin shinkafar wadanda aka girbe.