Boko Haram sun kashe manoma 40, wasu sun ɓace a Borno
An shiga ruɗani a yankin bayan faruwar harin.
Ana zargin mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla manoma 40 a Ƙaramar Hukumar Kukawa, a Jihar Borno.
Harin ya faru ne a ranar Lahadi, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma a kauyen Kayakura, yankin Doron Baga.
- Yadda muka kashe manyan yaran Bello Turji —Sojoji
- NAJERIYA A YAU: Yadda jiragen soji suka kashe fararen a karo na biyu a wata guda
Har yanzu ba a gano wasu manoman ba, bayan harin.
Wannan harin ya faru ne kwana ɗaya bayan wani hari a Chibok, inda aka kashe mutum biyu tare da ƙone wata coci.
Wani mazaunin yankin ya ce ’yan ta’addar sun zo ne da yawa sannan suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa.
“A halin yanzu, mutane da dama sun ɓace kuma sama da manoma 40 aka kashe, mafi yawansu sun tsere ne daga hare-haren da aka kai a Ƙaramar Hukumar Gwoza,” in ji shi.
Sai dai wani jami’in tsaro a yankin ya ce adadin waɗanda suka mutu ya kai 30.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Kenneth Daso, ya ci tura, domin ba a same shi a waya ba.