Boko Haram sun kashe mutum 375 bana- Kungiyar Amnesty
Kungiyar Amnesty International (AI) ta ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutuum 375 bana a hare-hare 55 da suka kai a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Kungiyar ta ce watan da ya fi muni shi ne watan Agusta, lokacin da ‘yan ta’addan suka kashe mutum 100, mai biye mishi kuwa shi ne watan Nuwamba, […]
Kungiyar Amnesty International (AI) ta ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutuum 375 bana a hare-hare 55 da suka kai a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Kungiyar ta ce watan da ya fi muni shi ne watan Agusta, lokacin da ‘yan ta’addan suka kashe mutum 100, mai biye mishi kuwa shi ne watan Nuwamba, inda tun yanzu an kashe mutum 76.
A jawabin da ya yi, daraktan kungiyar na Najeriya, Osai Ojigho na nuna rashin jin dadinsa a harin Mubi na ranar Talatar da ta gabata, inda akalla mutum 59 suka rasa rayukansu.
Ojigho ya ce Harin ya zo ne ‘yan kwanaki kadan bayan sata da kisan gillar da aka yi wa manoma 6 a kauyen Dimge, Karamar Hukumar Mafa a Jihar Borno.