Boko Haram sun kashe sojoji 9 a harin ba-zata da suka kai sansanin soji a Borno
Maharan sun kai harin yayin da tsaka da maka ruwan sama da sanyin safiyar ranar Juma’a.
Aƙalla sojoji tara ne suka rasa rayukansu bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hari wani sansanin soji da ke Mandara-Girau, a Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce harin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Juma’a yayin da ake ruwan sama mai ƙarfi.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun zo da yawa tare da ƙaddamar da harin ba-zata kan sojojin da ke sansanin.
Majiyoyin sun bayyana cewa sojoji tara sun rasu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin.
Haka kuma, maharan sun mamaye wani ɓangare na sansanin sojin.
Wani bidiyo da Aminiya ta samu ya nuna gawarwakin sojoji takwas da aka rufe da wani mayafi kwance a ƙasa.
Ƙauyen Mandara-Girau yana da tazarar kilomita kaɗan daga garin Biu.
Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.