Boko Haram sun sake kashe mutum 10 a Adamawa

Mayakan Boko Haram sun sake kashe mutum 10 a kauyen Kwamda-Kobla da ke karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa a hari na biyu da suka kai karamar hukumar. Rahotanni sun ce akalla ’yan bindiga 20 ne suka kai harin kauyen da misalin karfe 5:00 na safe a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka kashe […]

Boko Haram sun sake kashe mutum 10 a Adamawa
Boko Haram sun sake kashe mutum 10 a Adamawa

Mayakan Boko Haram sun sake kashe mutum 10 a kauyen Kwamda-Kobla da ke karamar Hukumar Madagali a Jihar Adamawa a hari na biyu da suka kai karamar hukumar.

Rahotanni sun ce akalla ’yan bindiga 20 ne suka kai harin kauyen da misalin karfe 5:00 na safe a ranar Juma’ar da ta gabata, inda suka kashe wasu mazaje da wukake da gaturra. Shugaban karamar Hukumar Madagali, Ularamu Maina ya ce ’yan bindigar a wannan karon ba su kashe mutane da bindiga ba face yanka su.
Ya ce ’yan banga sun bi ’yan bindigar cikin daji ko za su samu nasarar kamo su, amma ba su same su ba. “kauyen na nan akalla kilomita biyar daga Guyuk, babu tsaro a wurin domin sojojin da ke wurin an kai su cikin garin Madagali da Guyuk,” inji shi.
Mazauna kauyen sun ce yanzu ’yan bindigar ba su cika kai hari da bindiga ba domin karancin bindigogi da suke fama da su, sai dai su shiga kauyuka su tada wa mutane hankali.
A wani labarin kuma an sake wa mata da yara 275 da aka ceto daga dajin Sambisa kuma aka kai su Makolhi da ke Yola a ranar 2 ga Mayu, 2015 an kai su wani boyayyen wuri.
A lokacin da Aminiya ta ziyarci sansanin ’yan gudun hijira na Makolhi ba kowa, inda wata majiya ta ce mata da yaran sun bar Makolhi ne a cikin dare ranar Talata da Larabar makon jiya.
Wani mazaunin wurin ya ce sojoji ba su bada dalilin kwashe su ba, amma an kwashe 200 cikin dare ranar Talata sauran kuma ranar Laraba. “Sojoji sun zo da motoci suka fara kwashe su, koda muka tambayi dalilin kwashe su, sai suka ce umarni ne daga sama. Sai suka yi maza suka kai su filin jirgin Yola a motocin suka shiga jirgin suka bace,” inji shi.
Wata majiyar ta ce ana zargin wasu daga cikin matan suna waya da ’yan Boko Haram cikin dare. “Kuma ana ganin idan har ba a yi bincike a kai ba, hakan zai iya janyo babbar matsala ga tsaron wurin,” inji majiyar.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Hukumar NEMA, Sani Datti, ya ce ya san da kwashe su, amma ba zai kara wani abu a kan haka ba, domin wannan harkar sojoji ne.