Boko Haram sun yanke kawunan mutum 5 a Borno
Idan an tuna cewa mutane 416 aka sace a jihar Borno da ƙarfin bindiga.
Rahotanni sun bayyana cewa, ’yan Boko Haram sun yanke kawunan mutane biyar daga cikin mutane 416 da aka sace daga cikin al’ummar Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Wani bidiyo da ’yan Boko Haram suka tura ta kafofin sada zumunta a ranar Laraba ta hannun wata ƙungiyar sulhu, ƙungiyar matasa ta Borno ta Kudu, an ga ƙungiyar ’yan ta’addan, Jama’atu Ahlis-Sunna Lidda’awati wal-Jihad da aka fi Sani da Boko Haram suna rera waƙa yayin da take nuna gawarwakin waɗanda suka kashe.
- Mashigar Hormuz a buɗe take ga wasu ƙasashe — Iran
- Sojoji sun kama mutum uku da ake zargi da satar shanu
An fitar da bidiyon na daƙiƙa 30 bayan wani wa’adin sa’o’i 72 da aka bayar ga gwamnatin tarayya.
Idan an tuna cewa mutane 416 aka sace a jihar Borno da ƙarfin bindiga.
Sun kuma yi gargaɗin cewa, idan ba a biya musu buƙatunsu cikin sa’o’i 72 ba, za a mayar da waɗanda abin ya shafa zuwa wurare da ba a bayyana ba inda ba za a sake ganinsu ba.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar laraba, shugaban ƙungiyar matasan Borno ta Kudu, Samaila Kaigama ya ce waɗanda abin ya shafa sun yi yunƙurin tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane.
Sanarwar da ke tare da bidiyon ta ce: “ƙungiyar Matasan Borno ta Kudu (BOSYA) jiya, da misalin ƙarfe 5:18 na yamma, ta sami wani bidiyo mai tayar da hankali wanda ke nuna kisan gillar da aka yi wa maza kimanin huɗu zuwa biyar, manya da yara, waɗanda aka ruwaito sun yi yunƙurin tserewa ne daga hannun ’yan Boko Haram ɗin.”
Kaigama ya ce ƙungiyar ta binciki dukkan hanyoyin da za a iya bi wajen taimakawa da kuma hanyoyin jin ƙai, duk da haka mata, yara da wasu maza 416 da ke hannun ’yan Boko Haram an bar su a hannunsu.
“Wannan bidiyon ba an yi shi ne don yaɗa ta’addanci ko wani aiki da ya shafi hakan ba, a’a, don fallasa gaskiyar da ke faruwa a ƙasa, gaskiyar da muka shafe sama da watanni biyu muna ƙoƙarin hana ta ta hanyar ci gaba da yin sulhu da kuma roƙon jin ƙai,” in ji shi.
Don haka ƙungiyar matasan kudancin Bornon ta yi kira ga ’yan Najeriya masu kyawawan halaye da su goyi bayan ƙoƙarin ceto waɗanda abin ya shafa.
“ƙungiyar Matasan Borno tana kira ga ’yan asalin Kudancin Borno masu kishin ƙasa, masu riƙe da muƙamai na siyasa, masu neman takarar siyasa, da dukkan ’yan Najeriya masu kishin ƙasa daga Arewa, Kudu, Gabas da Yamma, da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da su gaggauta tallafawa ƙoƙarin da ake yi na sakin mata da yara 416,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Mutane huɗu zuwa biyar sun riga sun mutu. An ƙara samun waɗanda abin ya shafa suna rashin lafiya, kuma an kashe wasu maza da suka yi ƙoƙarin tserewa.”
Ya jaddada cewa, akwai rayuka a cikin lamarin kuma waɗanda abin ya shafa suna fuskantar mawuyacin hali a lokacin da ake garkuwa da su.
“Don Allah mu haɗu mu bayar da gudummawa don tara N50,000,000 don sakin mata da yara 50,” in ji shi.
Za a tuna cewa a makon farko na watan Maris 2026, Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ƙungiyar ta kai hari kan sansanin sojoji a Ngoshe, ta ƙone motocin aiki, ta tarwatsa jami’an tsaro ta kashe mutane da ba a fayyace adadinsu ba, sannan ta sace wasu da dama.