Boko Haram Ta Ba Mazauna Yankunan Borno 8 Kwanaki 3 Su Tashi

Jin hakan ke da wuya mazauna yankunan suka tattare suka koma garin Benishiekh, hedkwatar karamar hukumar Kaga

Boko Haram Ta Ba Mazauna Yankunan Borno 8 Kwanaki 3 Su Tashi

’Yan ta’adda da ake zarin mayakan Boko Haram ne sun ba da wa’adin kwanaki uku ga al’ummomin wasu guundumomi takwas a Karamar Hukumar Kaga ta Jihar Borno da su tattare ya nasu ya nasu su bar yankunan ko su yaba wa aya zaki.

Wata majiya a Maiduguri ta ce, jin hakan ke da wuya mazauna yankunan suka tattare suka koma garin Benishiekh, hedkwatar karamar hukumar a ranar Talata.

Mazauna yankunan sun ce ’yan ta’addan sun zarge su da ba tsegunta wa jami’an tsaro kan hare-haren da suka akai a baya-bayan nan da suka halaka da wasu ’yan ta’addan a yankin.

“Mutanenmu suna tserewa daga gidajensu kasancewar ’yan ta’addan ba su da nisa da hanyar Maiduguri zuwa Damaturu saboda zargin mutanen kauyen suna sane da kasancewarsu a yankunan nasu,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa, mutanen yankunan na tsoron ’yan ta’addan za su iya kai farmaki kansu a kowane lokaci shi ya sa suka yanke shawarar tserewa da rayukansu.

A wani labarin kuma, an kashe mutane uku a lokacin da wasu ’yan ta’adda suka kai hari a wani kauye da ke karamar hukumar Konduga a Jihar Borno.

Lamarin da ya afku a yammacin Lahadin da ta gabata ya haifar da fargaba a kauyen da kuma makwabtansa.

Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda  bayan da ’yan ta’adda sun kai hari ga tawagar Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni a kan hanyarsu ta komawa Damaturu gaga Maiduguri a yammacin Asabar inda aka kashe wani  dan sanda, wasu bakwai kuma suka samu raunuka

Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji

Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano

Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi

Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara