Boko Haram ta banka wa gari wuta a Borno

Akalla fararen hula biyar ne kungiyar Boko Haram ta kashe a hare-haren da ta kai a jihar Borno. Mayakan kungiyar sun banka wa kauyuka wuta da tsakar dare bayan sun ci karfin mazauna a karamar hukumar Konduga. Da daren Lahadi ne maharan suka far wa kauyen Kondori inda suka kashe mutum hudu suka kuma sa […]

Boko Haram ta banka wa gari wuta a Borno

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Akalla fararen hula biyar ne kungiyar Boko Haram ta kashe a hare-haren da ta kai a jihar Borno.

Mayakan kungiyar sun banka wa kauyuka wuta da tsakar dare bayan sun ci karfin mazauna a karamar hukumar Konduga.

Da daren Lahadi ne maharan suka far wa kauyen Kondori inda suka kashe mutum hudu suka kuma sa wa kauyen wuta.

“Yanzu haka babu kowa ya tsere saboda sun kona kauyen kurmus.

“A take suka harbe mutum uku suka jikkata wasu hudu. Mutum na hudun shi ma ya rasu,” inji ‘yan sintirin yankin.

A wani hari da mayakan suka kai karamar hukumar Jere, sun banka wa sakatariya wuta suka kuma kwashi wasu kayan yaki.

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Taraba

Jami’an NSCDC sun daƙile harin ’yan bindiga a Kano

Matsalar Tsaro: Ku sayi makamai don kare kanku — Sarkin Argungun

Mai juna biyu na wata 8 ta shigar da ƙarar neman saki