Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a Kamaru

A shekaranjiya Laraba ne jama’ar garin Kouyafe da ke karamar Hukumar Kolofata a lardin Arewa-mai-Nisa na kasar Kamaru suka tashi  da firgici saboda wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin garin lokacin da ake sallar asubah. Harin wanda na farko ne a wannan gari, ya hallaka rayukan jama’a 13 cikinsu har da limamin […]

Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a Kamaru
Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare a Kamaru

A shekaranjiya Laraba ne jama’ar garin Kouyafe da ke karamar Hukumar Kolofata a lardin Arewa-mai-Nisa na kasar Kamaru suka tashi  da firgici saboda wani harin kunar bakin wake da aka kai masallacin garin lokacin da ake sallar asubah.
Harin wanda na farko ne a wannan gari, ya hallaka rayukan jama’a 13 cikinsu har da limamin masallacin.
Masallacin wanda aka gina shi da tubali ya tarwatse baki daya. Kakakin Gwamnati Minista Issa Tchiroma Bakary ya ce wani matashi ne dauke da damarar abubuwan fashewa ya doshi masallacin da su.
Kodayake, har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin hakan. Amma tuni hukumomi  a kasar suka jingina harin da kungiyar Boko Haram. Ganin cewa a baya can ita ce ta ke kai hare-hare a wannan yankin hadi da garkuwa da jama’a kamar yadda ya kasance a bara, lokacin da ‘yan kungiyar suka yi garkuwa da uwar gidan Mataimakin Firaministan Kamaru Amadou Ali tare da wasu danginsa.
Garin Kouyafe na da tazarar kilometa 10 da Kolofata.