Boko Haram ta kai sabon hari a Benishiekh
Maharan suna mayar da hankalinsu zuwa wurin da aka kashe Birgediya Janar O.O. Braimah a makon jiya
A karo biyu kasa da mako guda ’yan ta’addan Boko Haram sun sake kai hari a garin Benishiekh da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, lamarin da ya haifar da fargabar tsaro a yankin.
An ruwaito cewa maharan suna mayar da hankalinsu zuwa ga rundunar sojoji ta 29 ta Operation Hadin Kai, wurin da aka kashe Birgediya Janar O.O. Braimah a makon jiya.
An kuma ga wasu daga cikin ’yan ta’addan a sassan garin, lamarin da ya kara tsorata mazauna yankin.
A cewar majiyoyin yankin, an lura da wasu mutane da ake zargi ’yan ta’addan suna zirga-zirga a kan babura a kusa da yankin a ’yan kwanakin baya.
Wata majiya daga al’umma ta ce irin wannan zirga-zirga galibi suna nuna shirye-shiryen kai hare-hare na dare, yayin da mayakan ke barin baburansu nesa kafin su ci gaba da tafiya zuwa inda suke so.
Duk kokarin da aka yi don tuntubar kakakin rundunar OPHK Laftanar Janar Sani Uba game da sabon harin ya faskara.