Boko Haram ta kama mayakan ISWAP 60 a Borno
’Yan Boko Haram 78 sun mika wuya ga sojoji, an kashe mayakan ISWAP da Boko Haram 100 a cikin mako guda
Boko Haram ta cafke kwamandojoji da mayaka 60 na abokiyar gabarta, kungiyar ISWAP, a yayin da kungiyoyin biyu suka kashe wa juna mayaka sama da 100 a cikin mako guda.
Manyan kwamandojin ISWAP da suka fada a tarkon Boko Haram a hanyarsu ta zuwa Damasak da ke Jihar Borno daga Tafkin Chadi a ranar Litinin su ne Abubakar Saddiq, Abou Maimuna da kuma Malam Idris.
- Mu muka harbo jirgin sojin Najeriya —Dogo Giɗe
- Yanzu-yanzu: Mutum 2 sun mutu a turereniyar karbar sadaka a Kano
Majiyar Zagazola Makama, kwararre a kan sha’anin tsaro da yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, ya ruwaito cewa a baya-bayan nan bangaren Buduma na kungiyar Boko Haram ya kwace wasu sansanoni tare da fatattakar mayakan ISWAP a yankunan Kukawa da Madayi da kuma Kwatan Mota.
“Nasarar da suke samu kan ISWAP a baya-bayan nan na da nasaba da yadda wasu fusatattun mayakan ISWAP ke komawa bangaren Buduma na kungiyar Boko Haram,” a cewarsa.
Zagazola ya ruwaito cewa “Boko Haram ta tsare mayaka da kwamandojin na ISWAP a kurkukunta na karkashin kasa da ke Kwatan Mota, daura da Dogon Chukwu a matsayin fursunonin yaki.”
’Yan Boko Haram 78 sun yi ‘saranda’
A gefe guda kuma, wasu mayakan Boko Haram 78 tare da iyalensu sun mika wuya ga dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta Najeriya a Karamar Hukumar Monguno ta Jihar Borno.
’Yan Boko Haram din sun mika wuya ne bayan sojoji sun tsaurara ragargazar maboyarsu da kuma rikicin cikin gidan kungiyar ISWAP, wanda ya yi sanadiyyar kashe mayaka sama da 100 a cikin mako guda.