Boko Haram ta kashe Hafsan Soji ta kwace sansanin sojoji a Borno

An kasa dauko gawar wadanda mayakan suka kasa, saboda tsananin fadan da aka gwabza da misalin karfe 1 da dare

Boko Haram ta kashe Hafsan Soji ta kwace sansanin sojoji a Borno

Sojojin Najeriya a filin fareti. (Hoto: Twitter/HQNigerianArmy)

Mayakan Boko Haram sun kashe wani hafsan soja da wasu ’yan sa-kai biyu a wani ƙazamin hari a sansanin sojoji a Jihar Borno.

Wata majiyar soji ta shaida mana cewa an kasa ɗauko gawar waɗanda aka kashe, saboda tsananin faɗan da aka gwabza da misalin ƙarfe 1 na dare a sansanin da ke yankin Krenowa a Ƙaramar Hukumar Marte ranar Asabar.

Ta ƙara da cewa maharan sun lalata wata motar yaƙi, amma direbanta ya tsira da rauni a ƙafarsa, sannan sojoji fiye da 100 tare da makamai da sauran kayan aikinsu sun janye zuwa garin Marte.

Ƙoƙarinmu na jin ta bakin kakakin Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa, Manjo-Janar Edward Buba, ya faskara.

Mun kira wayarsa amma ba ta shiga, sannan har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton ba mu samu amsar rubutaccen saƙon da aka tura masa ba.

Amma wasu majiyoyi sun shaida mana cewa mayaƙan Boko Haram sun kai wa sojojin hari ne kwanaki biyar bayan sojojin sun ƙwace sansanin ƙungiyar da ke Krenowa a ƙoƙarin sojojin na kakkaɓe ’yan ta’adda.

Wani soja ya shaida wa wakilinmu cewa, “mun kai musu hari muka ƙwace sansaninsu, amma daga baya suka kawo mana harin kwanton ɓauna, dole muka janye.

“Ina kyautata zaton ɓuya suka yi, saboda babu wata alamar shirin harin kwanton ɓauna.

“A ƙarshe dai sansanin rundunar  27 Task Force da ke garin Marte muka koma,” in ji majiyar sojin.