Boko Haram ta kashe jama’a ta ƙona gidaje a Yobe

Mayaƙa sama da 50 ɗauke da muggan makamai ne suka far wa ƙauyen suna kisan gilla da kone-kone suna wawushe kayayyaki

Boko Haram ta kashe jama’a ta ƙona gidaje a Yobe

Yadda Gobara ta lakume Babbar Kasuwar Nguru a Yobe

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun hallaka mutane da dama, suka ƙona gidaje da kantuna tare da wawushe kayayyaki a ƙauyen Mafa da ke Ƙaramar Hukumar Taruwa ta Jihar Yobe.

Mayaƙa sama da 50 ɗauke da muggan makamai a kan babura ne suka far wa ƙauyen a yammacin ranar Lahadi.

Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan Sanda a Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ne ya tabbatar da harin a Damaturu a safiyar Litinin.

DSP Dubgus ya ce shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa “Zuwa yanzu ba mu tantance adadi rayukan da aka rasa ba, a harin da aka kai da misalin karfe 4 na ranar Lahadi.

“Wani daga ƙauyen Mafa ne ya kai rahoton harin ne a Babban Ofishin ’Yan Sanda na Ƙaramar Hukumar Tarmuwa.

“Mayaƙan, dauke da manyan makamai har da RPG sun far wa gundumar Mafa, suka ƙona gidaje da kantuna.

“Sun kuma kashe mutane da dama, amma ba a kai ga tantance adadinsu ba,” in ji DSP Dungus.

Ya ƙara da cewa maharan sun kuma jefar da wasu takardu masu ɗauke da rubutun Larabci.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa