Boko Haram ta kashe ma’aikaciyar agaji Hauwa Leman
Wani bangare na ‘yan kungiyar Boko Haram ISWAP sun kashe ma’aikaciyar agaji Hauwa Leman ma’aikaciyar kungiyar agaji ta Red Cross ICRC. An dai yi garkuwa da Hauwa tare da wasu jami’an kiwon lafiya tun a watan Maris na 2018 a garin Rann dake jihar Borno. Wata daya da gabata ne aka kashe Saifura Ahmed sakamakon […]
Wani bangare na ‘yan kungiyar Boko Haram ISWAP sun kashe ma’aikaciyar agaji Hauwa Leman ma’aikaciyar kungiyar agaji ta Red Cross ICRC.
An dai yi garkuwa da Hauwa tare da wasu jami’an kiwon lafiya tun a watan Maris na 2018 a garin Rann dake jihar Borno. Wata daya da gabata ne aka kashe Saifura Ahmed sakamakon rashin amincewar da ‘yan kungiyar suka yi da hukumomin Najeriya na kin cika masu bukatunsu.
‘Yan kungiyar dai sun fitar da bidiyon kashe Hauwa Leman kafin sanarwar.