Boko Haram Ta Kashe Magina Ta Sace Mafarauta A Yobe

Wasu mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu masu aikin gini biyu tare da yin garkuwa da mafarauta uku a gidan hakimin garin Kukaretra da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe. Basaraken ya ce ’yan ta’addan da suka kai hari da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadin sun shafe […]

Boko Haram Ta Kashe Magina Ta Sace Mafarauta A Yobe

Wasu mahara da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe wasu masu aikin gini biyu tare da yin garkuwa da mafarauta uku a gidan hakimin garin Kukaretra da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe.

Basaraken ya ce ’yan ta’addan da suka kai hari da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadin sun shafe awa guda suna harbe-harbe, suka kona gidan nasa na motarsa, sannan suka kashe wasu daga cikin bakin nasa, suka sace wasu, a gidan da kan titin zuwa Maiduguri.

Hakimin garin, Alhaji Lawan Babagana, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa ’yan ta’addan “Da misalin karfe 3 na asubahin ranar Lahadi suka kawo farmaki wannan gari namu suka rika harbe-harbe, suka banka wa gidana wuta, suka kona motata kirar Peugeot 504, sannan suka lalata gida daya a garin.

“Mutane biyar ne a gidana, wadanda masaukin bakina ne; biyu daga cikinsu ma’aikatan gine-gine ne da Hukumar Raya Arewa maso Gabas ta kawo daga Adamawa, domin gina Kasuwar Kukareta.

“Kamar yadda kuka sani a matsayina na sarkin gargajiya, nakan karbi bakuncin mutanen da ke zuwa yankina; Wadannan yara  mayakan Boko Haram ne, sun fito da wadannan ma’aikatan daga gidana, suka harbe su nan take.

“Akwai mafarauta guda uku, wadanda nake karbar bakunci a gidana, inda wadannan ’yan ta’adda suka daure, suka yi garkuwa da su a cikin motar ’yan banga da aka ajiye a gidana,” Inji shi.

“’Yan sanda sun kwashe ragowar ma’aikatan ginin tare da kai su asibitin kwararru da ke Damaturu don duba lafiyarsu,” in ji shi.

Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taro a Saudiyya

Zaɓen Ondo: Atiku ya gargaɗi INEC kan tafka maguɗin zaɓe

Sojoji sun tafka ƙazamin artabu da Bello Turji a Sakkwato 

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa