Boko Haram ta kashe manoma da masu sana’ar itace 18 a Borno

Ana ci gaba da bincike domin gano inda sauran mutane suke, yayin da ake fargabar wasu na hannun ‘yan ta’addan.

Boko Haram ta kashe manoma da masu sana’ar itace 18 a Borno

Taswirar Jihar Borno

Ana fargabar cewa wasu mayaƙan Boko Haram sun kashe manoma da masu sana’ar itace 18 a yankin Gwoza da ke Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyoyi sun ce harin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da mayaƙan suka yi wa manoman kwanton ɓauna da ke kan hanyarsu ta zuwa gyaran gonaki gabanin damina.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa mayaƙan sun riƙa buɗe wuta kan duk wanda aka gani a hanyar, lamarin da ya jawo asarar rayuka da dama.

Wani ma’aikacin jarida a ƙaramar hukumar Gwoza, Malam Haruna Hayatu, ya tabbatar da cewa an gano gawawwakin mutane 18 daga cikin daji.

Sai dai ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano inda sauran mutane suke, yayin da ake fargabar wasu na hannun ‘yan ta’addan.

Haka kuma, Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ya samu kiran gaggawa a safiyar ranar Alhamis ɗin dangane da faruwar lamarin.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan mamatan ya kuma bai wa iyalansu haƙurin jure wannan rashi.