Boko Haram ta kashe mutane fiye da 400 a Kamaru – Rahoto
A shekaranjiya Labara ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta wallafa wani rahoto game da kisan rayukan jama’a da kungiyar Boko Haram ta yi a tsakanin bara zuwa bana a yankin arewacin kasar Kamaru. Rahoton ya bayyana cewa rayukan daruruwan jama’a sun hallaka ba gaira ba dalili, fiye da tsofaffi 130 da […]
A shekaranjiya Labara ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta wallafa wani rahoto game da kisan rayukan jama’a da kungiyar Boko Haram ta yi a tsakanin bara zuwa bana a yankin arewacin kasar Kamaru.
Rahoton ya bayyana cewa rayukan daruruwan jama’a sun hallaka ba gaira ba dalili, fiye da tsofaffi 130 da kuma yara maza sun bace ba tare da an ji duriyarsu ba. kungiyar ta zargi sojin Kamaru da kungiyar Boko Haram da tafka barna. Ta ce Boko Haram ta kashe fararen hula akalla 400 da kuma sojoji da dama a wannan shekarar.
Hakazalika, akwai mutane dubu daya ne a hannun hukuma ba tare da sun san makomarsu ba, a dalilin zargensu da ake yi cewa suna da alaka da Boko Haram. Game da haka Daraktan yankin Afirka ta Tsakiya da kuma ta Yamma na Amnesty International Alioune Tine ya ce, bai kamata a aiwatar da komai ba bisa ga hujjar cewa ana yaki da ta’addanci
Ya kara da cewa bisa ga hujjar yaki da ta’addanci bai kamata da ajiye yara kanana a gidan wakafi ba har fiye da watanni shida. Ya ce “ba daidai ba ne da ajiye mutanen da ake zargi da aikata wani laifi har na tsawon lokaci ba tare da an gurfanar da su ba a gafan kotu ba har ya kaiga wasu suna mutuwa a gidan yari,” inji shi.