Boko Haram ta kashe sojoji 6 a Chibok

Mayakan kungiyar sun kai harin ne da yamma a kan a sansanin sojin Najeriya.

Boko Haram ta kashe sojoji 6 a Chibok

Akalla mutum 7 ne suka mutu ciki har da sojoji, baya ga wadanda suka ji rauni, a harin da kungiyar Boko Haram ta kai wa sansanin soji da ke kudancin Jihar Borno.

Mayakan kungiyar sun kai harin a sansanin sojin da ke Kuda, daura da garin Chibok, inda suka kashe soja shida, suka kuma raunata wasu mutum takwas.

Wani daga cikin ’yan bangar garin mai suna Yohanna Bitrus, ya ce ’yan ta’addar sun kone gidaje sama da 40, sannan suka kwashe kayan abinci  da dabbobi tare da yin awon gaba da mototci uku.

“Sannan sun kone wata mata har ta mutu a cikin gidanta,” inji Bitrus.

Wata majiya daga rundunar sojin ta ce a ranar Lahadi Boko Haram ta kai musu harin, har ta kashe musu sojoji shida, sannan ta raunata wasu.

Kauyen Kuda na da tarzarar kilomita 3 ne da cikin garin Chibok, a jihar ta Borno.

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta

Sojoji sun daƙile yunƙurin mayaƙan ISWAP a Borno