Boko Haram ta kashe sojoji 6 a Nijar
Ma’aikatar Harkokin cikin Gidan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa wasu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne sun kashe sojojin kasar shida, kuma sun jikkata wasu sojojin uku.Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gidan da aka karanta a gidan rediyon gwamnati shekaranjiya Laraba ta ce, ‘yan Boko Haram din sun yi wa sojojin kwanton bauna […]

Ma’aikatar Harkokin cikin Gidan Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa wasu da ake zaton ‘yan Boko Haram ne sun kashe sojojin kasar shida, kuma sun jikkata wasu sojojin uku.
Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gidan da aka karanta a gidan rediyon gwamnati shekaranjiya Laraba ta ce, ‘yan Boko Haram din sun yi wa sojojin kwanton bauna ne yayin da suke sintiri a kusa da garin Diffa, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wurin da lamarin ya auku yana da nisan kilomita 20 da iyakar Nijar da Najeriya.
‘Yan Boko Haram sun sha kai hare-hare a yankin Diffa, inda a baya suka kashe mutane da dama.
Yankin na Diffa yana kusa da iyakar Najeriya da Nijar.
A watan Disambar bara mazauna kauyen Gamgara da ke Jihar Diffa sun ce wasu da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka mutane shida a wani hari da suka kai kauyen.
Rahotanni sun ce an kone yawancin gidaje, kuma ana zargin sun gurbata ruwan rijiyar kauyen da guba, saboda kumfar da ya ke ta yi.