Boko Haram ta kashe wani shugabanta kan yunkurin yin tawaye
Kungiyar ta kashe shugaban nata kan zargin shirin yi mata tawaye
Boko Haram ta kashe daya daga cikin shugabanninta mai suna Amir Jaysh, Abou Hassana, bisa zargin tawaye da nufin kafa wani sabon bangare daga cikin kungiyar.
An kashe Abou Hassana ne tare da wasu mutum uku da ake zargi da laifin tawayen a gaban wasu mayaka a tsaunin Mandara da ke Karamar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.
Aminiya ta rawaito cewa Ali Ngulde, Shugaban Boko Haram na biyu mafi girma ne, ya bayar da umarnin kashe su bayan an yanke musu hukuncin kisa kan laifukan da suka aikata.
A cewar majiyoyi, Abou Hassan na kokarin tayar da wani bangare mai zaman kansa a cikin kungiyar Boko Haram domin jagorantar ta’addancin nasa a kauyen Koltafirgi da aka fi sani da Gaizuwa a Sambisa.
Majiyar Zagazola Makama, kwararre kan harkokin tsaro sun ce tuni an maye gurbinsa da Alhaji Ari Hajja Fusam, dan asalin garin Bama da ke jagorantar ‘yan ta’addan Boko Haram a Gaizuwa kafin sojojin Najeriya su fatattake su bayan sun yi asara mai yawa.
Alhaji Ari Hajja Fusam da Ba’a Issah sun samu karin girma zuwa Amir yayin da Bakura Jega tsohon Nakib, ya samu karin girma zuwa Khaid.
Muke dan shekara 33, Khaid na Dutsen Mandara, Ali Ghana, Khaid na Ngauri, dake Arewacin Banki, Abbah Tukur, da Abu Isa, za su ci gaba da rike mukaminsu na Khalid kamar yadda majiyar ta bayyana.
Idan za a tuna, kungiyar Ali Ngulde Boko Haram ta yi mummunar asarar mayakanta da kayan aiki daga sojojin Najeriya a Grazah da Wa-Jahode, a gefen tsaunin Mandara a kwanakin baya.