Boko Haram Ta Kwace Yankunan Borno ta Arewa —Shugaban Majalisa

Shugaban majalisar ya ce Boko Haram na rike da wasu yankunan kananan hukumomin jihar guda biyu

Boko Haram Ta Kwace Yankunan Borno ta Arewa —Shugaban Majalisa

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdulkarim Lawan, ya ce a halin yanzu, Boko Haram na rike da ikon yankunan kananan hukumomi biyu a jihar.

Abdulkarim Lawan ya nuna damuwarsa kan dawowar ayyukan Boko Haram, duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta dage cewa babu wani yanki a jihar da ya rage a hannun ’yan ta’addar.

Shugaban majalisar ya ce a halin da ake ciki, yankunan kananan hukumomin Guzamala da Kukawa a yankin Borno ta Arewa suna karkashin ikon ’yan ta’addar ne.

Lawan wanda shi ne wakilin Guzamala a Majalisar Dokokin jihar, ya yi wadannan banyan ga manema labarai ne a ranar Lahadi.

Ya yi kira ga sojoji da su kara himma tare da kwato yankunan da lamarin ya shafa daga Boko Haram don maido da zaman lafiya a cikinsu.

An yi garkuwa da mutum 43 da kashe yaro a Sakkwato

Klopp zai maye gurbin Nagelsmann a matsayin kocin Jamus

Sojoji sun kama masu ƙera makamai a Kebbi

Bam ya kashe aƙalla mutum shidda a Siriya