Boko Haram ta sace matafiya a hanyar Maiduguri-Kano

Mayakan Boko Haram sun sace matafiya a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Boko Haram ta sace matafiya a hanyar Maiduguri-Kano

Cunkoso a hanyar Kaduna-Abuja

Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi garkuwa da matafiya a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.

Kawo yanzu ba a tantance yawan matafiyan da kungiyar ta sace ba a harin na ranar Litinin.

Maharan sun far wa matafiyan ne a tsakanin kauyen Garin Kuturu da Mannanari da ke makwabtaka da Auno a kan babbar hanyar Damaturu.

Majiyoyin tsaro sun ce sace fasinjojin da aka yi a yammacin ranar Litinin ya tilasta wasu matafiya komawa garuruwan Benishek da Auno, a yayin da wasu suka makale a wurin da abin ya faru.

“Abin ya faru ne a tsakanin Mannanari da Garin Kuturu inda mayakan Boko Haram suka tare motoci suka yi awon gaba da fasinjojinsu.

“Ba mu san adadin wadanda aka sace ba, amma ranar Litinin da yamma abin ya faru,” a cewar wata majiyar tsaro.

Wani mazaunin Auno mai suna Banna Kwomi ya ce motocin haya da dama sun tsere daga wurin da abin ya faru suka dawo Auno.

Ya bayyana cewa ’yan Boko Haram sukan addabi al’ummomin kauyukan Garin Kuturu da Mannanari.

A wannan karon “sun fito ne da baro guda uku, da alamar kayan abinci suka fito nema, amma ba mu san mutane nawa aka dauke ba.

“Amma direbobin motocin haya da dama sun dawo nan Auno, sai daga baya da aka turo sojoji suka motocin suka koma suka wuce zuwa Maiduguri,” in ji Banna Komi.

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji