Boko Haram Ta Sake Lalata Turakun Wutar Lantarki Mai Karfin 330KVA A Yobe
Mayaƙan Boko Haram sun sake lalata turakun wutar lantarki mai karfin 330 KVA, lamarin da ya jefa mazauna jihohin Yobe da Borno cikin duhu
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ce wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun sake lalata wasu turakun wutar lantarki mai karfin 330 KVA, lamarin da ya jefa mazauna jihohin Yobe da Borno cikin halin duhu kamar yadda ya faru a watannin baya.
Kakakin rundunar, Dungus Abdulkarim ya shaida wa ’yan jarida cewa maharan sun yi amfani ne da abubuwan fashewa wajen lalata turakun da suka dauko wutar lantarkin daga Gombe zuwa jihohin Yobe da Borno.
Ya ce “Wadannna turakun wutar lantarkin suna nan ne a kusa da kauyen Kasaisa da ke Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe.
“Wannan barna ta lalata turakun da ke dauke da wayoyin samar da hasken wutar lantarkin ya jefa mazauna jihohin biyu cikin duhu,” in ji shi.
- Biyan Kudin Hayar Zama Cikin Kabari
- ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta sanya wa Nijar albarkacin watan Ramadana
Aminiya ta ruwaito cewa harin da aka kai kan turakun shi ne na biyu cikin watanni uku.
Mahara sun lalata su a watan Disamba, amma aka gyara a watan Janairu, kafin yanzu da aka sake lalata su.