Boko Haram: Tsakanin yakin addini da na tattalin arziki
Tun lokacin da magoya bayan Malam Muhammad Yusuf suka bullo da salon wa’azinsu na haramta karatun zamani da muke kira karatun boko na rika zargin cewa wannan da’awa wani yunkuri ne na kasashen duniya domin kawo nakasu ga Musulmin Najeriya kuma kila wani shiri ne na hana hakar man fetur a yankin Arewa maso Gabas […]
Tun lokacin da magoya bayan Malam Muhammad Yusuf suka bullo da salon wa’azinsu na haramta karatun zamani da muke kira karatun boko na rika zargin cewa wannan da’awa wani yunkuri ne na kasashen duniya domin kawo nakasu ga Musulmin Najeriya kuma kila wani shiri ne na hana hakar man fetur a yankin Arewa maso Gabas musamman a Tafkin Chadi da ke cike da dimbin albarkatun mai da iskar gas.
Na rika kokarin nuna wa masu bin malamin cewa kada su kuskura su bari a yi amfani da addini a cutar da kasar nan, kada su yarda a fake da addini a bude kofar fitinar da mu da su ba za mu iya rufe ta ba, kuma kada su kuskura su jefa mu da su kansu a cikin bala’in da ba a san karshensa ba.
A galibin tattaunawata da daidaikunsu nakan nuna musu cewa an dade ana neman bata sunan Musulmin Najeriya a jingina su da ta’addanci kamar yadda ake jingina takwarorinsu na kasashen duniya. Ba na mantawa muhawara ta karshe da muka yi da daya daga cikinsu wanda yanzu nake tunanin ba ya raye, ita ce na nuna masa cewa, fakewa da tabargazar da wasu masana ilimin kimiyya ko sanin motsin abubuwa (Phesics) ta cewa haka kawai duniya ta samu kanta ba wanda ya yi ta, ba sa wakiltar ilimin zamani ko boko, illa iyaka dama can su maguzawa ne da suka samu ilimin don haka za su auna shi ne da fahimtarsu da tunaninsu. Kuma na taba shaida wa wani daga cikinsu cewa, shin mu Musulmi muna zuwa wurin Turawa ne su karantar da mu addini ko muna neman ilimin rayuwar duniya ce a wurinsu kamar kafinta da wanke gyambo da kanikanci da sauransu? Na ce masa babu wanda yake zuwa wurin irin wadancan Turawa ya nemi su koya masa Ahlari ko Risala ko Alkur’ani ko wani fanni na addini. Don haka mu je mu koyi sana’a a wurinsu ba laifi ba ne.
Kai akwai lokacin da na shaida wa wani daga cikinsu cewa, idan Bature ya ce ruwan sama tururi ne daga teku, to wane ne ya halicci tekun? Kuma da Allah Ya ce, Yana saukar da ruwa daga sama Ya ce, akwai wata kwarya ko matata ce da ke tara ruwan ya sauko? Kuma shin idan mutum ya hau jirgin sama ya tsallake ruwan ya zamo ruwan yana kasar jirgin, sai a ce ba ruwan sama ba ne? Sannan kasashen da ba su kusa da teku wa yake daukar ruwan saman ya kai musu? Na shaida musu cewa, ba mu ce tsarin ilimin ba ya da kuskure ba, tunda ba mu muka tsara shi bisa addininmu ba, amma su lura akwai ka’idar da ke cewa idan munanan abubuwa biyu suka hadu kuma ya zamo dole mutum ya dauki daya, to sai a dubi mafi dama-dama daga cikinsu a dauka don haka watsi da ilimin boko kamar yadda suke kira ya fi illa daga koyonsa.
Kuman na rika nanata musu cewa daukar makami da sunan yaki, bude kofar fitina ce da mu da su ba za mu ji dadi ba. Kuma na sha nuna musu kada su yarda a yi amfani da su wajen biyan bukatun makiya Najeriya saboda wannan yaki da ake son su shiga ba na addini ba ne, na tattalin arziki ne.
Tunanina a lokacin shi ne a hana hako man fetur a yankin Arewa maso Gabas da ya hada da Borno da Bauchi da Adamawa wadanda aka tabbatar suna da shi. Na yi musu tambayoyi da dama, a karshe da na fara jin suna cewa jinin duk wanda ya saba musu ya hallata, sai na ja bakina na yi gum na daina tanka musu.
Don haka harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a makon jiya suka kashe tare da sace wadansu ma’aikatan Jami’ar Maiduguri da suke aikin gano man fetur din ya tabbatar da tsoron da na rika nunawa a shekarun baya. Ina da yakinin wadanda suka haddasa yakin Boko Haram, sun yi haka ne saboda sun san babu abin da mutanen Arewa suka fi girmamawa da martabawa irin addini, su san cewa idan suka haddasa rikicin kabilanci ba za su samu nasara ba, idan suka zuga kasashen Chadi ko Kamaru su tayar da rikicin iyaka da Najeriya ba za su samu nasara ba. To me ya saura? Sai a yi amfani da dan gari domin a ci garin da yaki. Haka kuwa aka yi aka yi amfani da ’ya’yanmu aka nuna musu addini ake so a karfafa su kuma suka yarda suka bayar da rayuwarsu a kai, amma a can kasa, manufar ita ce a hana hako man fetur a Arewa maso Gabas, domin biyan bukatun wasu kasashen duniya da kuma ’yan kwangilarsu na nan Najeriya. Wannan lamari na sace masana masu binciken mai a kusa da kauyen Jibi ya fara fito da maitar wadanda suka assasa yakin Boko Haram din a fili.
Sai dai wani abu mai karfafa zukata shi ne da Shugaban Jami’ar Maiduguri Farfesa Ibrahim Njodi ya ce suna tare da Kamfanin NNPC game da neman danyen man da ake yi a tafkin Chadi kuma za su ci gaba da binciken duk da harin na Boko Haram.
Farfesa Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da Minista a Ma’aikatar Man fetur Dokta Ibe Kachikwu da wadansu manyan jami’an Kamfanin NNPC suka kai masa ziyara a karshen makon jiya, ya ce, “Mutanen jami’ar nan sun damu bayan harin da aka kai wa masu aikin neman mai ciki har da wadansu ma’aikatan jami’ar. Amma ba za mu janye daga aikin neman man ba. Muna tare da Kamfanin NNPC don a koma a ci gaba da aikin neman.”
Shi ma Kamfanin NNPC din ya ce za su ci gaba aikin neman mai a yankin Tafkin Chadin.
Wannan mataki abin karfafa gwiwa ne, bai kamata hukumomin kasar nan su mika wuya ga ’yan ta’adda kuma ’yan barandar wasu kasashe da suke neman hana Najeriya amfani da albarkar man da Allah Ya jibge a wani yankin nata ba.
Sanannen abu ne cewa galibin yake-yaken da muke gani yau a duniya, suna aukuwa ne saboda dalili na tattalin arziki koda kuwa an jingina su da addini ko kabilanci. Najeriya ba za ta kubuta daga irin haka ba, sai dai ya kamata wadanda ake amfani da su domin cimma wannan buri musamman ’yan Boko Haram su fara tunani cewa abin da suke yi ko kadan ba ya da alaka da Musulunci. Su lura an fake ne da addini ana sanya su suna tafka barna da zubar da jini marar amfani kuma Allah ba zai yarda da haka ba. Su yi wa kansu tambayoyi shin zuwa yanzu wane alfanu suka samar wa Musulunci da Musulmi bayan da suka dauki makami suka shiga kashe jama’a? Su tambayi kawunansu wane alfanu suka samar wa iyalansu a addinance da duniyance? Shin wanda yake neman daukaka Musulunci ya koma kashe Musulmi, anya Musulunci yake yi wa aiki ko wanin Musulunci? Ko ba a fada ba, kashi 95 na mutanen da ’yan Boko Haram suka hallaka Musulmi ne, to wace riba Musulunci ya samu bayan ana hallaka mabiyansa ana rugurguza dukiyarsu ana mayar da ’ya’yansa mata gwagware, ana mayar da dubban kananan yaransa marayu?
Su tuna wannan yanki da ya kunshi jihohin Borno da Yobe da suka fi aikata tu’annati, nan ne cibiyar Alkur’ani a Yammacin Afirka, yanzu sun ruguza wannan dama sun mayar da yankin kwata ta zubar da jini da sanya firgici a zukatan jama’a. Su tuna sun yi wa Musulunci da Musulmi barnar da za a dauki shekara-da-shekaru ba a gyara ba. Don haka abin da suke yi ya isa haka! Shugabannin bangarorin kungiyar Boko Haram, wato Abubakar Shekau da Al-Barnawi da Ansaru su ji tsorn Allah su tuna duk digon jinin da ya zuba a dalilinsu za su yi bayani a gobe kiyama. Su tuna jihadi ko kitali yana da ka’idoji da sharudda a karkashin koyarwar Musulunci, ba haka kawai mutum zai ci abinci ya koshi ya ayyana jihadi ko yaki ba.
Ga gwamnati da hukumomin tsaro muna yaba kokarinsu na magance ta’addancin Boko Haram, amma muna rokonsu su fi mayar da hankali wajen samun bayanan sirri kan kungiyar da mayakanta, maimakon bayar da fiffiko wajen amfani da karfi. Muna bukatar a kawo karshen zubar da jinin da ake yi a Arewa maso Gabas cikin gaggawa. Da jama’ar gari da sojoji da mayakan Boko Haram da ake hallakawa duk asara ce ga kasar nan. Don haka a samo maslaha ta lumana domin kasar nan ta huta.
Ga Kamfanin NNPC, mun yaba da ya ce zai yi duk abin da zai iya don ganin ya tallafa wa Jami’ar Maiduguri da iyalan mutanen da mayakan Boko Haram suka sace a makon jiya. Kuma muuna jinjina ga Farfesa Ibrahim Njodi kan alkawarta ci gaba da aiki da Kamfanin NNPC don ci gaba da binciken makamashin da ke jibge a yankin Tafkin Chadin.