Boko Haram: Wajibi ne shugabannin Arewa su farka – ACF
Tsohon Sufeto Janar na’Yan sandan Najeriya kuma Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) Alhaji Ibrahim Coomassie ya bukaci shugabannin Arewa su tashi don magance kalubalen tsaro da ke fuskantar yankin. Alhaji Ibrahim Coomassie, ya ba da wannan shawarace a wurin taron gaggawa na kungiyar da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da aka gudanar a Kaduna a […]
Tsohon Sufeto Janar na’Yan sandan Najeriya kuma Shugaban kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) Alhaji Ibrahim Coomassie ya bukaci shugabannin Arewa su tashi don magance kalubalen tsaro da ke fuskantar yankin.
Alhaji Ibrahim Coomassie, ya ba da wannan shawarace a wurin taron gaggawa na kungiyar da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da aka gudanar a Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.
Ya ce matsalar tsaro da ayyukan kungiyar Boko Haram suka haifar babbar abar dubawa ce a tarihin kasar nan. “Wajibi ne mu ceto Arewa da kuma kasar nan, kuma nasararmu za ta kawo kyakkyawar fata da girmamawa da hadin kai da kuma hadin gwiwa a Arewa,” inji shi.
Ya ce idan shugabannin Arewa suka gaza ceto Arewa, dukkanmu tarihi zai bayyana mu da wani rukunin shugabannin da suka sayar da makomar ’ya’ya da jikokinsu.
Tsohon shugaban ’yan sandan ya bukaci shugabannin Arewa su rika magana da murya daya inda ya ce: “Wajibi ne mu rika magana kamar iyalin Arewa ba a matsayin kungiyoyi ko daidaikun mutane ba.”
Alhaji Coomassie ya ce Arewa tana karkashin mamaya inda ake kai mata hare-hare ta kowane gefe. “A Borno da Adamawa da Yobe ana yanka ’ya’yanmu, ana yi wa mata fyade ana sace wasu, ana karkashe wasu,” inji shi.
Ya nuna damuwa kan yadda wasu garuruwa a Arewa maso Gabas suka koma karkashin ikon mahara, inda ya ce hatta sarakuna da shugabannin addini maharan bas u kyale ba.