‘Boko Haram: ’Yan Arewa ku nisanci kwana a wuraren Ibada’

Majalisar sarakunan Arewa ta jihar Legas ta gargadi ’yan Arewa mazauna jihar su guji kwana a masallatai da coci-coci da gine-ginen da ba kammala ba da kuma karkashin gadojin jihar don gudun fadawa tarkon ’yan kungiyar boko haram.Gargadin ya zo a daidai lokacin da kungiyar boko haram ta dauki alhakin  harin bom din da aka […]

‘Boko Haram: ’Yan Arewa ku nisanci kwana a wuraren Ibada’
‘Boko Haram: ’Yan Arewa ku nisanci kwana a wuraren Ibada’

Majalisar sarakunan Arewa ta jihar Legas ta gargadi ’yan Arewa mazauna jihar su guji kwana a masallatai da coci-coci da gine-ginen da ba kammala ba da kuma karkashin gadojin jihar don gudun fadawa tarkon ’yan kungiyar boko haram.
Gargadin ya zo a daidai lokacin da kungiyar boko haram ta dauki alhakin  harin bom din da aka kai a jihar a makon da ya gabata wanda jami’an tsaro suka ce motar da ke dauke da gas ce ta fashe
Shugaban majalisar sarakunan Arewa kuma Sarkin Hausawan Legas, Alhaji Sani Kabiru shi ne ya yi furucin yayin wani taron manema labarai da majalisar sarakunan ta kira wanda aka yi a gidan Arewa da ke unguwar Ebute-Meta a Legas a karshen makon da ya gabata. Sarkin ya ce ‘Dalilin da ya sa muka nemi jama’a su guji kwana a wuraren Ibada da gine-ginen da ba kammala ba shi ne kwanakin baya an kama ’yan Arewa da dama, wadansu an kama su yayin da suke salla a masallatai, wasu yayin da suke kwance a gine-ginen da ba a kammala ba, wasu ma suna tafiya a ka kama su, mun sha wahala kwarai da gaske wajen ceto wadanda aka kama. Kuma bisa la’akari da halin da ake ciki a yanzu shi ne muka dauki nauyin fadakar da mutanenmu muhimmancin kiyayewa don kada su fada tarkon bata-gari’.
Ya ci gaba da cewa ‘Wani dalilin kuma shi ne muna ganin cewa a kwai bata-gari da ke amfani da masallatai da coci-coci suna yada munanan akidu, saboda haka muke kira ga mutanenmu duk inda suka ga ana yin irin wannan abu su nisanci wuri. Kuma muna kira ga mutanenmu su nisanci ajiye ababen hawa a kan manyan hanyoyi da wuraren kasuwanci, domin yin hakan zai iya bai wa bata-gari damar yin mugun abu’.
Ya ce harin bam din da aka kai a jihar Legas wata alama ce da ake so a musgunawa ’yan Arewa da ke zaune a Legas.
“E haka ne ai ka ga kamar misali musgunawar ba a Legas ba ne kawai, amma abin da yake faruwa a yanzu saboda kalubalen tsaro da ake fuskanta ba za mu fito karara mu ce mu aka nufa ba, dole sai an bi yadda aka ce a yi tun da farko, sannan mu gane rashin adalcin da aka yi sai mu kuma mu yi korafi, amma a yanzu idan ka ce za ka yi korafi ba kada wata hujja saboda su jami’an tsaro ne mu kuma fararen hula ne to amma idan suka ci gaba da kame babu kakkautawa kuma idan muka je beli muka ga abubuwan da suke faruwa, ka ga muna iya korafi a lokacin,’ inji shi.
Ya dage a kan cewa ba sa dardar da matakan da jami’an tsaro suke dauka kan al’amuran da suka shafi inganta tsaro a jihar.
‘Ba dardar muke yi ba muna goyon baya ne. Ka gane shi ya sa muke aiki tare da su  saboda kalubalen tsaro da ake ciki’.
Sai dai ya yi kira ga jami’an tsaro su hada kai, kuma su rika magana da yawu daya a duk lokacin da aka samu matsala a harkar tsaro a jihar.
‘Rashin hadin kai a tsakanin jami’an tsaro yana ba mu mamaki, shi da kansa kwamshinan ’yan sanda ya gaya mana cewa wacce ta kai harin bom din mace ce  ’yar Arewa don a kafarta an ga lalle  to yaya  wasu kuma za su ce ba bom ba ne bayan su da kansu ’yan boko haram din sun fito sun ce su ne suka kai harin. Ka ga irin wannan yana janyo matsala’.
Shi kuwa Sakatare Janar na majalisar sarakunan Arewa, Alhaji Garba Chede ya yi kira ga ’yan Arewa su yi katin rijista dan jiha da gwamnatin jihar take yi.
‘Muna kira ga mutanenmu su tabbatar cewa sun karbi katin gwamnatin jihar Legas, don idan aka kama mutum ba shi da wannan kati ba za mu iya karbo shi ba, don ba mu da shaidar da za ta nuna mana cewa shi mazaunin Legas ne,’ in ji shi.
Shi ma Sarkin kabilar Shuwa Arab, Sultan Jibril Yahaya ya yi kira ga ’yan Arewa su zama masu bin doka da oda a jihar.