Boko Haram: Za a kashe Dala bilyan biyu don tallafa wa yankin Arewa maso gabas

A makon da ya gabata ne aka gudanar da wani taron gangami na yadda za a tallafa wa mutane da ma yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wadanda yakin Boko Haram ya daidaita, inda hukumomin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da dai sauran masu ruwa da tsaki a yankin suka hallara, a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban […]

Boko Haram: Za a kashe Dala bilyan biyu don tallafa wa yankin Arewa maso gabas
Boko Haram: Za a kashe Dala bilyan biyu don tallafa wa yankin Arewa maso gabas

A makon da ya gabata ne aka gudanar da wani taron gangami na yadda za a tallafa wa mutane da ma yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wadanda yakin Boko Haram ya daidaita, inda hukumomin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da dai sauran masu ruwa da tsaki a yankin suka hallara, a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo.

Alhaji Muhammad Sani Zoro, dan Majalisar Wakilai ne daga Jihar Jigawa kuma shi ne yake shugabantar kwamitin kula da ’yan gudun hijira a majalisar. Yayin day a kasance daya daga cikin mutanen da suka halarci wannan taro bayyana cewa: “Wannan taron zai taimaka wajen aza harsashin yadda za a agaza wa wannan yanki da al’ummarta, na yadda suka kwashe tsawon shekaru shida suna fama da hare-haren ta’addanci; na yadda kowane bangaren rayuwa ya samu nakasu, kama daga harkar ilimi, kiwon lafiya, noma, kasuwanci da samar da ababen more rayuwa, gami kuma da lalacewar muhalli da hukumomin gwamnati. To wannan shi ne makasudin shirya wannan taro kuma an kiyasta za a kashe sama da Dala biliyan Biyu, don a kawo masu waraka daga mawuyacin halin da suka shiga. Su ma su ci gaba da rayuwarsu kamar kowa tare da fatan Allah Ya kawo karshen wannan bala’i.”
Zoro ya ci gaba da cewa: “Wannan taro, ina gani ya dauki tafarki na samun nasara a kan manufofin da aka sa a gaba. Da farko dai an sami tsari wanda zai hada kawunan hukumomin gwamnati da kungiyoyi saboda kada idan an zo bayar da wannan tallafi ko kuma taimaka masu ta wata fuskar, wata kungiyar ta yi gabas, wata kuma ta yi arewa; a yayin da kuma gwamnati ke nata bangaren. Saboda haka an sami daidaito don a tafi kan tsari daya kuma alkibla daya, yadda kowa zai san aikin da kowa yake yi.”
Da ya juya ga mutanen da aka yi wannan taron domin su, shugaban kwamitin lura da ’yan gudun hijirar ya ce wasu gwmnatocin kamar na Borno tuni suka ma fara tsara yadda za a mayar da su gidajensu, a akasarin kauyukansu saboda ana ganin an fara samun kwanciyar hankali. Ya kara da cewa, ko su ma kansu jami’an tsaro suna nasu iya kokarin wajen gyaran hanyoyi da gadoji da sauransu, ganin an sami daidaito wajen komawarsu kauyukansu. Akwai kuma maganar cewa gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen dakile wannan ta’addanci. Za a yi iya kokari wajen kiyayewa da mutanen da abin ya shafa kai tsaye, ta fuskar gyara masu muhallansu da samar masu da abinci da ababen more rayuwa, tare da kula da marayun yaransu da gwagwaren matansu.