…Boko Haram za ta iya kwace Jihar Borno – Rahoto

Wani rahoton kwararru ya yi gargadin cewa watakila Najeriya ta rabe biyu saboda yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da karbe iko da wasu yankunan Arewa maso Gabas.Rahoton da kungiyar Najeriya Security Network ta fitar, ya ce kungiyar Boko Haram a shirye take ta kwace Maiduguri babban birnin Jihar Borno bayan harin da ta […]

…Boko Haram za ta iya kwace Jihar Borno – Rahoto
…Boko Haram za ta iya kwace Jihar Borno – Rahoto

Wani rahoton kwararru ya yi gargadin cewa watakila Najeriya ta rabe biyu saboda yadda kungiyar Boko Haram ke ci gaba da karbe iko da wasu yankunan Arewa maso Gabas.
Rahoton da kungiyar Najeriya Security Network ta fitar, ya ce kungiyar Boko Haram a shirye take ta kwace Maiduguri babban birnin Jihar Borno bayan harin da ta kai a Bama.
kungiyar ta ce “Idan har garin Maiduguri ya fada hannunsu, nasara ce mai muhimmanci kuma alama ce ta karfin Boko Haram.”
Kungiyar kwarrarrun wacce ta hada da tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Cambell, ta ce samun nasara a hare-haren zai ba Boko Haram damar kwace daukacin Jihar Borno da kuma watakila wasu sassan jihar Adamawa da Yobe har zuwa kasar Kamaru.
Rahoton ya ce, “Dole ne a dauki matakin da ya dace, idan ba haka ba wani yanki mai fadi na Najeriya zai koma hannun Boko Haram kamar yadda kungiyar IS ta yi a kasar Iraki.”
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta gaggauta tura karin sojoji zuwa Maiduguri domin hana garin fadawa hannun abokan gaba, kuma gwamnati ta kwato wasu hanyoyin Jihar Borno domin katse hanzarin ’yan Boko Haram.
Ta ce rashin kwarin gwiwa da rashin makamai na daga cikin abubuwan da ke hana sojoji murkushe Boko Haram, kuma suke gudu daga fagen daga.
Rahoton ya bukaci kasashen waje su kawo wa Najeriya dauki musamman da kayayyakin soji.
Rahotanni sun nuna cewa a yanzu haka Boko Haram ne ke iko da garuruwan Gwoza da Limankara da Dikwa da Damboa da Gamborou Ngala, da Buni Yadi a Jihar Yobe, da Madagali a Jihar Adamawa.

An fara sana’ar hayar Fawa-bank a Kano

’Yan sanda sun kama fasinja ya ɓoye bindiga a cikin burodi 

An kama fasto kan kashe ’yar shekara 13 da duka

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya