Boko Haram: Zulum ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe gudummawar N300m

Gwamna Zulum ya buƙaci sojoji su ƙara zage damtse wajen ganin sun kawar da ragowar mayaƙan Boko Haram a faɗin yankin tafkin Chadi.

Boko Haram: Zulum ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe gudummawar N300m

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 300 don tallafawa iyalan sojojin da suka rasa rayukansu a yaƙin da ake yi da mayaƙan Boko Haram.

Zulum ya bayyana hakan ne a garin Njemena na ƙasar Chadi, yayin da halarci bikin karrama dakarun sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu don kare ƙasar na (MNJT Operation Desert Sanity 2 Medal Parade) na shekarar 2025 a ranar Laraba.

Ya ce, za a bayar da gudummawar ne ta wata gidauniya mai suna “Tribute to Our Troops Charity Foundation,” wanda ke da nufin karrama mazan jiya da suka mutu a fagen daga, da karrama maza da mata da suka yi fafutuka don ganin an ci gaba da tabbatar da kare martabar iyakokin Nijeriya da kuma kai tallafi ga iyalan da suka bari.

“Shugaban hafsan tsaron ya kafa wata gidauniya da za ta duba rayuwar iyalan sojojin da suka mutu da kuma waɗanda suka samu raunuka a wajen aikin tsaro.

“Ba abin da za mu iya fiye da wannan; sun sadaukar da rayukansu don kare martabar ƙasa. Za mu ci gaba da tallafa musu. Na yi farin ciki da kafa irin wannan gidauniya. Idan har akwai wata jiha a Najeriya da ya kamata ta ba da gudummawa wajen tallafawa wannan gidauniya, to Borno ce,” in ji shi.

Gwamnan ya ce, duk da ƙalubalen da ake fuskanta na tashe-tashen hankula a yankin Arewa maso Gabas sun ragu matuƙa.

Ya buƙaci sojoji su ƙara zage damtse wajen ganin sun kawar da ragowar mayaƙan Boko Haram a faɗin yankin tafkin Chadi.

Faretin da aka yi da bada lambar yabo ta MNJTF da aka fara gudanarwa a shekarar 2017, na karrama sojojin da suka sadaukar da kai da kuma yaba musu da jajircewar sojoji da kwamandojin yaƙi da mayaƙan Boko Haram a ƙasashen da ke kewayen tafkin Chadi.

Zulum ya bayyana godiyarsa ga shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa na yaƙi da rashin tsaro a yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan ƙasar nan.