Boko Haram:Najeriya za ta sayo jiragen leken asiri
Ministan Harkokin Cikin Gida Mista Abba Moro, ya ce Gwamnatin Tarayya tana shirin sayo jiragen sama na leken asiri uku don sanya ido a kan ayyukan ’yan kungiyar Boko Haram.Minista Moro ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai, inda ya ce gwamnati za ta dauki matakin ne da zimmar yakar ta’addanci da sauran […]
Ministan Harkokin Cikin Gida Mista Abba Moro, ya ce Gwamnatin Tarayya tana shirin sayo jiragen sama na leken asiri uku don sanya ido a kan ayyukan ’yan kungiyar Boko Haram.
Minista Moro ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai, inda ya ce gwamnati za ta dauki matakin ne da zimmar yakar ta’addanci da sauran manyan laifuffuka da ’ya’yan kungiyar Boko Haram da haramtattun bakin haure suke yi a kasar nan.
Mista Moro ya ce, “A ziyarar da na kai kwanakin baya zuwa Jamhuriyar Czech, mun je wuraren da ake sayar da jirage marasa matuka a Prague, kuma mun mika shawararwari ga hukumomin gwamnatin da lamarin ya shafa domin su sayo jirage uku. Da zarar mun samu amincewar yin hakan za mu sayo su.”
Sai dai Mista Moro bai bayyana adadin kudin da za a kashe wajen sayo jiragen ba, kuma bai fayyace ko an sanya su a cikin kasafin kudin kasar nan ba bana ba.
Wani wakilin gidan rediyon BBC, Landan ya ce Najeriya tana kokarin tattaunawa da hukumomin kasar Kamaru domin kulla wata yarjejeniya ta yadda dakarun Najeriya za su iya kai hari a sansanin ’yan Boko Haram da ke cikin kasar ta Kamaru.
A kwanakin baya Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya kaddamar da wani jirgi mara matuki a Kaduna, sai dai wasu bayanai sun nuna cewa har yanzu jirgin bai fara aiki ba.
kasar Amurka na amfani da irin wadannan jirage marasa matuka a kasashen Pakistan da Afghanistan domin zakulo wadanda take kira ’yan ta’adda, sai dai sau da dama hare-haren da suke kaiwa na fada wa kan fararen hula da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.