Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa

Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa da kuri’a 8,794,726.

Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa

Dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu, ya zama zababben shgaban kasar Najeriya.

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar a safiyar Laraba, 29 ga watan Maris, 2023, cewa Tinubu na Jm’iyyar APC mai mulki ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar 25 wata.

“Kasancewar ya cika sharudda kuma ya samu kuri’u mafi rinjaye a zaben, Bola Tinubu shi ne ya yi nasara,” in ji Farfesa Yakubu.

Bayan tattara sakamakon zaben, Yakubu ya sanar cewa Tinubu ya yi nasara a kan sauran abokan takararsa da kuri’u 8,794,726.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ne ya zo na biyu da kuri’a 6,984,520.

Dan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Anambra ya zo a matsayi na uku da kuri’a 6,101,533 a yayin da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya samu kuri’a 1,496,687 a matsayin na hudu.

Tun kafin a kai ga sanar da sakamakon zaben na karshe dai jam’iyyun PDP da LP da wasu suka yi fatali da shi, bisa zargin magudi da saba dokar zabe, inda suka ce za su shigar da kara a gaban kotu.

Sai dai kuma daga cikin jam’iyyu 18 da ake da su a Najeriya, 11 sun nesanta kansu da boren da PDP ta jagoranta na ficewa daga cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasar da ya gudana a Abuja.

Farfesa Mahmood Yububu ya bayyana cewa ’yan Najeriya 93,469008 ne ke da katin zabe kuma an tantance 25,286,616 daga cikinsu a zaben na ranar Asabar.

Daga cikin adadin, mutum 24,965,218 ne suka kada kuri’a, inda aka samu sahihan kuri’u 24,025,940 da kuma guda 939,278 da suka lalace.

Da nasarar da Tinubu ya yi, INEC za ta mika zai karbi takardar shaidar zama zababben shugaban kasar Najeriya — na biyar a Jamhuriya ta hudu, wadda ta fara a shekar 1999, lokacin da kasar ta sake dawowa mulkin dimokuradiyya.

Za a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, a matsayin zabebben shugaban kasar Nariya na 7 kuma shugaba na 16, tun bayan samun ’yancin kasar a 1960.

Ya ci zabe ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki sakamakon sauyin wasu takartun kudin kasar na Naira da kuma dokar takaita amfani da tsabar kudi da gwamnati mai ci ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Wata matsalar da take ci wa Najeriya tuwo a kwarya ita ce ta karancin man fetur, rashin tsaro da kuma rashin abubuwan more rayuwa.