Bom din ’yan bindiga ya kashe fasinjoji 12 a Zamfara

Karo na biyu ke nan cikin mako guda fasinjoji suke rasuwa bayan motocin haya suke ciki sun taka bom din da ‘yan ta’adda suka dasa a Jihar Zamfara

Bom din ’yan bindiga ya kashe fasinjoji 12 a Zamfara

Wasu ’yan bindiga a Najeriya.

Ana fargabar rasuwar wasu mutum 12 bayan fashewar wani abu da ake kyautata zaton bom ne da ’yan bindiga suka dasa a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

Abun fashewar da ake zargin nakiya ce, ya tashi ne bayan wata bas din haya mai dauke da fasinjoji 18 zuwa garin Dansadau ta bi ta kansa da misalin karfe 8.30 na safiyar ranar Laraba nan.

Karo na biyu ke nan cikin mako guda fasinjoji suke rasuwa bayan motocin haya suke ciki sun taka bom din da ‘yan ta’adda suka dasa a Jihar Zamfara