Bom din ’yan ta’adda ya kashe sojoji a Sakkwato
Sojojin sun gamu da ajalinsu a hanyarsu ta zuwa kai wa al’ummar Bargaja dauki sakamakon harin da ’yan ta’adda suka kai a cikin talatainin dare kafin wayewar garin Asabar
Kimanin sojoji biyu ne ake zargin sun rasu, wasu da dama suka jikkata bayan wani abin fashewa ya tashi motar a yankin Bargaja da ke Karamar Hukumar Isa ta Jihar Sakkwato.
Shaidu sun bayyan wa wakilinmu cewa kafin wayewar garin Asabar ne sojoji suka gamu da ajalinsu a yayin da suke hanyarsu ta zuwa kai wa al’ummar Bargaja dauki sakamakon harin da ’yan ta’adda suka kai a cikin talatainin dare, inda suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa waklinmu cewa ’yan ta’addan sun kai harin abin fashewan ne a kan hanyar Isa-Bargaja kafin sojoji su isa wurin.
“A hanyar sojoji na zuwa ne motarsu ta gamu da abin fashewan, kuma ya shafi sojoji da dama. Daya daga cikin sojojin ya shigo kauyenmu da mummunan rauni a kafarsa yana neman dauki,” in ji shi, yana mai bayyana damuwa game da salon da ’yan ta’adda suka dauko na amfani da ababen fashewa wajen kai hari.
- Matashi ya rasu a gidan budurwarsa a Kano
- Katsina: Sojoji sun ceto wanda aka sace, sun lalata sansanin ’yan bindiga
- Mahafiyar Kachalla Battujo za ta shekara 20 a gidan yari
Ya bayyana cewa, “Mun ga gawar sojoji biyu, amma ba mu san ko akwai karin wasu ba,” yana mai kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro a yankin.
Wani mazaunin yankin da ya yi ikirarin cewa shi da wasu mazauna yankin sun je sansanin sojoji da ke garin Isa suka yi musu ta’aziyya. “Mun dauki hayar motoci biyu daga yankinmu zuwa Isa inda muka yi wa sojojin ta’aziyyar abokan aikinsu da suka rasa,” a cewarsa.
Amma ya ce sojoji uku ne suka rasu a harin, ciki har da direban motar, kuma an dauke gawarwakin zuwa Sakkwato, babban birnin jihar.
Wata majiyar ta ce ’yan ta’adda sun kai wa sojojin hari ne a yayin da suke kan hanyar kai dauki bayan samun kiran neman taimako.
A cewar, “Sai da ’yan ta’addan suka bari motar sulke (APC) da ke jagorantar jerin gwanon motocin sojojin ta wuce sa’annan bude wa Hilux din da ke baya wuta da bindigogi, suka tayar da abun fashewa.”
Sai da majiyar ta ce soja daya ne ya rasu a yayin da wasu shida suka samu raunuka a harin, kuma ana neman wani daga cikin sojojin da ya shige cikin jeji a cikin duhun daren.
A cewarta, an yi musayar wuta tsakanin mazauna da sojoji da kuma ’yan ta’adda a tsawon daren, lamarin da ya haifar da tashin hankali a fadin yankin.
“Jiya mun kasa barci saboda karar harbe-harbe. Ba zan iya sanin hakikanin adadin wadanda abin ya rutsa da su ba yanzu, sai zuwa anjima, idan muka tattara bayanai,” a cewar majiyar.
Kokarin wakilinmu na samun bayani da sojoji bai yi nasara ba, har zuwa lokacin da ya turo wannan labarin.
Ya kira kakakin ’yan sanda na Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufai, amma jami’in bai amsa kiran ko rubutaccen sakon da aka aika masa ba kan harin.
Ya kuma kira Shugaban Karamar Hukumar Isa, Sharehu Abubakar Kamarawa, amma wayarsa ba ta zuwa kuma bai ba da amsar sakon WhatsApp da Tes da aka tura masa ba, har muka kammala wannan rahoton.