Bom ya kashe almajirai 4 da wasu 2 a Borno
Abun fashewan ya tashi ne a cikin wani kango da ke kusa da tsangayar almajiran
Wani abun fashewa ya kashe wasu kananan yara almajirai hudu da wasu manya biyu a Karamar Hukumar Gubio a Jihar Borno.
Shugaban karamar hukumar, Mali Gubio, ya ce abun fashewan ya tashi ne a cikin wani kango da ke kusa da tsangayar almajiran a safiyar ranar Asabar.
“ِAn gano gawar kananan yara almajirai hudu da wasu manya biyu, amma har yanzu ba a kai ga gano ’yan uwansu ba
“Dukkansu sun rasu, saboda baka ba za mu iya fadin hakikanin abin da ya faru ba, amma dai abun fashewa ya tashi a wani gida da ake ajiye kayan gwangwan,” in ji s hugaban karamar hukumar.
- An yanke mazakutar malamin allo daf da aurensa a Zariya
- An kama matar da ta sayar da kananan yara 42
A cewarsa, wasu na zargin ’yan bola-jarin sun dauko abun fashewan bisa rashin sani ne suka hada da kayan da suka tara a kangon da ke kusa da tsangayar.
Shugaban karamar hukumar ya kuma jaddada umarnin Gwamna Babagana Umara Zulum, na haramta ayyukan ’yan bola-jari a jihar, da nufin hana sace-sace kayan gwamnati a wuraren da mutane suka kaurace wa.