Bom ya kashe masu saran ice 7 a Borno

Masu saran ice bakwai sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan sun taka nakiya a yankin Konduga da ke Jihar Borno.

Bom ya kashe masu saran ice 7 a Borno

An yi jana’izar mamatan da suka riga mu gidan gaskiya.

Aƙalla masu saran ice bakwai sun rasu, wasu da dama sun jikkata bayan sun taka nakiya a yankin Konduga da ke Jihar Borno.

Shaidu sun bayyana cewa bom ɗin ya tashi da mutanen ne tsakanin ƙauyukan Masunfanari da Dogon Waya da ke kan babban titin Maiduguri zuwa Damboa.

Tsautsayi ya ritsa da su ne a safiyar Asabar, bayan motar a-kori-kura da suke tafiya a cikinta ta taka nakiyar da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka binne.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, “aƙalla mutane bakwai ne suka mutu nan take wasu da dama kuma sun jikkata a lokacin da abin ya faru da masu sauran ice a safiyar Asabar.

 

“A-kori-karar da suke ciki ta tashi aiki saboda tsananin fashewar nakiyar,” in ji majiyar.

Wani ganau, Bukar Modu, ya shaida wa Aminiya cewa ya ƙirga gawarwaki bakwai da aka kawo yankin Sulumari da ke daura da unguwar Masinrimari a birnin Maiduguri kafin a yi musu jana’iza.

Ya ce, “Gaskiya ne mutum bakwai sun rasu, cikinsu har da direban motar.

“An yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci a unguwar Masinrimari da ke Maiduguri da misalin ƙarfe 4 na yamma.”

Wakilinmu ya yi kokarin samun ƙarin bayani game da lamarin daga kakakin ’yan sanda a Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, amma hakan ya citura.