Bom ya kashe mutane 6, ya jikkata 7 a Zamfara

Wani ganau ya ce, ya ce abin fashewan ya tashi da wata mota ƙirar Golf wagon inda mutane 6 suka mutu nan take, wasu 7 suka tsira da raunuka daban-daba

Bom ya kashe mutane 6, ya jikkata 7 a Zamfara

Aƙalla mutane ne shida ne suka mutu, wasu da dama sun jikkata bayan wani abin fashewa da ’yan bindiga suka dasa ya tashi da mota mai ɗauke da fasinjoji da ke kan hanyar zuwa Bagega daga Anka a Jihar Zamfara.

Wani ganau wanda ya bayar da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya rutsa da su, Malam Shu’aibu, ya ce abin fashewan ya tashi da wata mota ƙirar Golf wagon inda mutane 6 suka mutu nan take, wasu 7 suka tsira da raunuka daban-daban.

Malam Shu’aibu ya ce, “Lamarin ya yi muni sosai, mutane 6 sun mutu nan take, wasu 7 kuma sun samu raunuka kuma aka kai su asibitin garin Anka.”

Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa, “Tashin wani abin fashewa da ’yan bindiga suka dasa a kan hanyar Bagega–Anka, jihar Zamfara, ya haifar da asarar rayuka da dama.”

Rundunar ta nuna damuwa kan yadda ’yan bindiga ke ƙara amfani da bama-bamai a hare-harensu.

“Tun daga watan Disamba, an samu ƙaruwa sosai wajen amfani da bama-bamai daga hannun ’yan bindiga. Wannan sabon lamari ya nuna yadda tsaro ke ƙara taɓarɓarewar a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda fararen hula ke ci gaba da shan wahala,” in ji rundunar.

Duk ƙoƙarin tuntuɓar Jami’in yaɗa Labarai na Rundunar Operation Fansa Yamma, Laftanar-Kanar Aliyu Danja, da kuma mai magana da yawun rundunar ’yan sanda ta jihar, DSP Yazid Abubakar, ya ci tura, domin ba su amsa kiran waya ba ko saƙonnin da aka tura musu.