Bom ya kashe ’yan sanda 3 a Zamfara
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya , Olatunji Disu, ya ce sadaukarwar da jami’an suka yi ba za ta tafi a banza ba.
Wasu jami’an ’yan sanda uku sun rasu bayan motarsu ta taka bam ɗin da ake zargin ’yan bindiga sun binne a kan hanyar Anka zuwa Bagega a Jihar Zamfara.
Jami’an, waɗanda ƙwararru ne wajen ganowa da lalata abubuwan fashewa, suna gudanar da sintiri ne lokacin da bam ɗin ya tashi da motarsu mai sulke.
- Ya kamata Netanyahu ya riƙa yin abu na masu hankali — Trump
- Tinubu ya amince a ɗauki jami’an tsaron dazuka 1,000 a Katsina — Dikko Radda
Rahotanni sun ce kafin faruwar lamarin, jami’an sun samu nasarar gano tare da lalata wasu bama-bamai da aka dasa a hanyar.
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa jami’an uku da lamarin ya rutsa da su sun haɗa da SP Abdulrazak Musa Hassan, Insfeta Auwal Ahmad da Insfeta Murtala Musa.
Da yake jajanta wa iyalan mamatan, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Disu, ya ce sadaukarwar da suka yi ba za ta tafi a banza ba, tare da alƙawarin ƙara matsa kaimi wajen yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.