Bom ya tashi a kasuwa a Yobe

An tabbatar da cewa wannan harin ba na kunar bakin wake ba ne.

Bom ya tashi a kasuwa a Yobe

Jihar Yobe

Wata fashewa da ake kyautata zaton bom ne ya tarwatse a babbar Kasuwar Shanu ta Buni Yadi da ke Karamar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Wani mazaunin Buni mai suna Bashar Direba ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na ranar yau Juma’a.

Kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kyaftin Shehu ya bayyana cewa an gano kuma wata nakiyar da aka dasa a kasuwar wadda sojoji suka yi nasarar warware ta jim kadan bayan fashewar ta farko.

Sai dai ya ce fashewar nakiyar ta farko ta rutsa da wata yarinya da ta samu mummunan rauni a kafarta, kuma yanzu haka tana karbar magani a daya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya da ke Buni Yadi.

Ya tabbatar da cewa wannan harin ba na kunar bakin wake ba ne sai dai an dasa bama-baman ne domin su hallaka mutanen da ba su ji ba ba su gani ba lura da cewar yau Juma’a ce cin kasuwar ta Buni Yadi.

Buni Yadi dai na da tazarar nisan kilomita 54 daga Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, inda har kawo yanzu yana fuskantar hare-hare lokaci zuwa lokaci

Wakilinmu ya ruwaito cewa shi ne garin da ya fi fama da hare-hare a Jihar Yobe da a baya ta shafe shekaru biyu a karkashin ikon mayakan Boko Haram.

Bayanai sun ce ana kyautata zaton har yanzu akwai burbushin mayakan na Boko Haram a wani sashi da ke da iyaka da Dajin Sambisa.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe