Boren sojoji: An tanadi shaidu 21 kan wadanda suka yi yunkurin kashe Janar
Rundunar Sojan Najeriya ta tanadi mutum 21 don ba da shaida a kan sojoji 18 da aka gabatar a gaban kotun soja bisa zargin yin bore a lokacin da suke aiki a Maiduguri tare da yunkurin kashe Babban Kwamandan Runduna ta Bakwai.Jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet wadda ta ruwaito labarin ta ce […]
Rundunar Sojan Najeriya ta tanadi mutum 21 don ba da shaida a kan sojoji 18 da aka gabatar a gaban kotun soja bisa zargin yin bore a lokacin da suke aiki a Maiduguri tare da yunkurin kashe Babban Kwamandan Runduna ta Bakwai.
Jaridar Premium Times da ke fitowa a intanet wadda ta ruwaito labarin ta ce daga cikin shaidun akwai Manjo Janar guda biyu da Birgediya Janar biyu da Kanar-Kanar uku da Laftana Kanar biyu da Manjo biyu da kuma Kyaftin uku.
Sauran shaidun sun hada da wani Laftana da mataimakan Laftana biyu da Masta Waran Ofisa daya da saje uku da kurtu daya. Kotun tana kuma da ikon kara kiran wasu shaidu idan bukatar haka ta taso.
Wata majiya ta ce sun boye sunayen shaidun ne saboda damuwar da ake nunawa cewa hakan na iya sanya rayuwarsu a cikin hadari kuma ya iya kawo cikas ga shari’ar da ake yi wa sojojin.
Kwamandan Sojojin Garison a hedkwatar soja B.T Ndioma ne ya kafa kotun a makon jiya don yi wa sojojin 18 shari’a kan zargin rashin biyayya ga manyansu da barazana ga rayukan kwamandojinsu tare da jawo takaddama a tsakanin sojoji.
Sojojin da za su gurfana a gaban kotun ana zargin sun yi tawaye tare da bude wuta ga motar Babban Kwamandan Runduna ta Bakwai da ke Maidguri a Jihar Borno, Manjo Janar Ahmadu Mohammed a ranar 14 ga Mayu, wanda aka yi masa sauyin wurin aiki bayan aukuwar lamarin.
Birgediya Janar C. C. Okonkwo ne zai jagoranci kotun don yi wa sojojin da suka zargi kwamandan da laifi a kashe abokan aikinsu a wani kwanton bauna da aka yi musu a kusa da Chibok inda aka sace kusan dalibai mata 300.
Jaridar Premium Times ce ta fara bayar da rahoton kafa kotun sojan, wanda rundunar sojan ta tabbatar daga baya a wani taron manema labarai da Kanar Onyema Nwachukwu da ya wakilci kakakin hedkwatar tsaro. Sai dai Kanar Nwachukwu bai fadi adadin sojojin da suke fuskantar tuhuma ba, kuma ya bukaci a kara hakuri za a bayyana wa jama’a halin da ake ciki.
Sojojin da ake zargin sun hada da Kofur Jasper Braidolor da Kofur Dabid Musa da Friday Onun da Yusuf Shuaibu da Igono Emmanuel dukansu masu igiya daidai. Sauran wadanda kurata ne sun hada da Andrew Ngbede da Nurudeen Ahmed da Ifeanyi Alukhagbe da Alao Samuel da Amadi Chukwudi da Allan Linus.
Sai Kofur Dabid Luhbut da Kofur Muhammed Sani da Stephen Clement mai igiya daya da Inama Samuel da Iseh Ugbong da Ichocho Jeremiah da Sabastine Gwamba.