Boren sojoji: Wasu sun janye, wasu sun cije
Boren sojoji ya dauki sabon salo, inda wadanda za su tafi Dalwa suka amince su tafi, saboda samun karin makamai, a yayin da wadanda za su tafi Bama da kuma Gwoza suka cije, suka ce ba za su tafi ba sai su nsamu karin ingantattun makamai.Wata majiya ta bayyana wa Aminiya har yanzu sojojin da […]
Boren sojoji ya dauki sabon salo, inda wadanda za su tafi Dalwa suka amince su tafi, saboda samun karin makamai, a yayin da wadanda za su tafi Bama da kuma Gwoza suka cije, suka ce ba za su tafi ba sai su nsamu karin ingantattun makamai.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya har yanzu sojojin da aka umarci su je Bama kafin su wuce zuwa Gwoza sun ce ba za su je ba har sai an ba su isassun makamai.
Idan ba a manta ba dai fiye mako biyu ne ’yan Boko Haram suka kwace iko da garin Gwoza, inda aka ci gaba da fafatawa don a kwace garin, amma abin ya ci tura.
A yanzu ’yan Boko Haram sun kwace fadar sarkin garin Gwoza bayan sun kafa tutocinsu a garin.
Wata majiya ta bayyana wa Aminiya an kara yawan sojoji da kuma makaman da za a tura Dalwa a shekaranjiya Laraba, kuma sun amince za su koma fagen daga.
“Nan da ’yan kwanaki kadan za kwato Dalwa da sauran kauyukan da ke kusa da shi.” Inji majiyar.
Aminiya ta gano sojojin da aka tura Bama kafin su wuce Gwoza har yanzu suna Maiduguri, sun ce sai an ba su ingantattun makamai.
Idan ba a manta ba sojoji da yawansu ya haura 30 sun ja tunga da motocinsu a kan hanyar Balabulin da ke Maiduguri bisa korafin cewa ba su da isassun makamai da harsasai da za su iya tunkarar mayakan kungiyar Boko Haram kuma ba za su yarda su yi mutuwar wulakanci ba.
Sojojin sun rika fadin cewa ko a ranar Litinin da ta wuce ’yan Boko Haram sun yi wa takwarorinsu kwanton bauna a kan hanya a hali ba su da makaman da za su iya mayar musu da martani.
daya daga cikin sojojin da suka yi boren, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya shaida wa gidan rediyon BBC Landan, cewa ba za su shiga daji ba, sai an ba su isassun kayan aiki da makamai.
Ya ce ba wai sun nuna rashin da’a ba ne da kin bin umarnin aikinsu na soja, “Abin ya yi yawa, yau dan uwanka ya fadi an kashe shi, gobe an kashe dan uwanka, gaba idan ka ga abin da ya fi karfinka ba sai ka jira umarni ba?” Ya nanata cewa cewa ’yan Boko Haram sun fi su makamai.
Ya yi zargin cewa akwai makamai a cikin barikin Maimalari, amma kwamandojinsu sun ki su fito da su. Ya ce saboda rashin makamai sun kasa zuwa sansanin Boko Haram a Alagarno, wanda bai wuce nisan kilomita takwas ba daga barikin Maimalari.
Sojan ya kara da cewa koyaushe a shirye suke su shiga daji domin yaki da Boko Haram idan aka ba su makamai.
Sai dai Kakakin Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Chris Olukolade ya ce ba su dauki wannan abu a matsayin bore ba, sai sun gudanar da bincike sun kuma tabbatar cewa haka ne, domin bore ba karamin laifi ba ne a aikin soja, kuma bai kamata a yi gaggawar cewa wani mataki da wani soja ya dauka ya kai ga matsayin bore ba, domin kuwa mugun laifi ne, kuma idan ba a an tabbatar da shi ba, ba za a yi shelar cewa bore ba ne.
Hafsan Hafsoshin Sojan Najeriya, Laftana Janar Kenneth Minimah ya yi barazanar korar matan sojoji daga bariki idan suka sake zanga-zanga kan tura mazansu fagen daga. Kuma ya gargadi sojojin cewa duk wanda ya yi bore zai fuskanci hukuncin bindigewa idan aka same shi da laifi.