Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

An ba su agajin gaggawa daga jami’an soji, sannan daga bisani aka miƙa su ga shugaban al’umma, Mallam Bulama Kunda, domin sake haɗuwa da iyalansu.

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai sun ceto mutane biyar da aka sace, ciki har da mata da yara, waɗanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su tun bayan harin da ta kai yankin Ngoshe a Karamar hukumar Gwoza, Jihar Borno.

A cewar majiyoyi, aikin ceton ya gudana ne a ranar 19 ga Yuni, 2026, da misalin ƙarfe 11:40 na dare, yayin wani sintiri da sojojin Bataliya ta 82 suka gudanar a yankin Bakasi.

Sojojin da ke sintiri sun hango mutane biyar suna yawo a dajin kusa da Ngoshe, kuma ana zargin sun tsere daga hannun ’yan ta’addan Boko Haram/ISWAP.

Binciken farko ya nuna cewa waɗannan mutanen mazauna garin Ngoshe ne, kuma an sace su ne a lokacin harin ta’addanci da aka kai yankin a ranar 3 ga Maris, 2026.

Waɗanda aka ceto su hada da Fatima Adamu, mai shekaru 80, Maryam Yakubu, mai shekaru 55, Abubakar Ibrahim mai shekaru 12, Musa Ibrahim, mai shekaru 11 da Fadima Adamu mai shekaru 8.

An ba su agajin gaggawa daga jami’an soji, sannan daga bisani aka miƙa su ga shugaban al’umma, Mallam Bulama Kunda, domin sake haɗuwa da iyalansu.

Sojojin sun jaddada cewa yanayin tsaro a yankin Arewa maso Gabas yana cikin kwanciyar hankali, sai dai ba a iya hasashen gaba.

Sun ƙara da cewa suna cikin shiri kuma suna ci gaba da gudanar da ayyukan yaƙi da ta’addanci yadda ya kamata.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland