Botsare wa APC” An ba hammata iska a majalisa

An dambace a Majalisar Dattawa inda aka samu tajin-tajin a Majalisar Wakilai bayan da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da magoya bayansu wadanda galibi sun fito ne daga jam’iyyar adawa ta PDP suka botsare wa umarnin jam’iyyarsu ta APC kan rabon sauran mukaman shugabancin majalisun biyu. A […]

Botsare wa APC” An ba hammata iska a majalisa
Botsare wa APC” An ba hammata iska a majalisa

An dambace a Majalisar Dattawa inda aka samu tajin-tajin a Majalisar Wakilai bayan da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da takwaransa na Majalisar Wakilai Yakubu Dogara da magoya bayansu wadanda galibi sun fito ne daga jam’iyyar adawa ta PDP suka botsare wa umarnin jam’iyyarsu ta APC kan rabon sauran mukaman shugabancin majalisun biyu.

A shekaranjiya Laraba ne aka dambace a Majalisar Dattawa saboda kin karanta sakon da Jam’iyyar APC ta aike wa shugaban majalisar Bukola Saraki kan raba sauran mukaman, yayin da a jiya Alhamis aka kasa zama a Majalisar Wakilai, lokacin da shugabanta Yakubu Dogara ya bi sahun Saraki wajen kin karanta wasikar da APC ta aike masa.
An yi ta iface-iface da kokarin sace sandar Majalisar Wakilan, kafin dogarin majalisar ya dauke ta. Dukkan majalisun biyu sun dare biyu, daya na goyon bayan umarnin Jam’iyyar APC kan wadanda za su cike sauran gurabun shugabancin majalisun, yayin da daya bangaren ke goyon bayan masu botsarerwar.
A Majalisar Wakilai rikici ya barke ne jim kadan da isowar shugaban majalisar, inda yana zaunawa wakilan APC suka fara gabatar da bayanan an keta wasu ka’idoji, sai wasu wakilan majalisar suka ruga don dauke sandar majalisar.
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Cif John Oyegun ya rubuta wata takarda ga shugabannin majalisun biyu inda ya jero sunayen wasu wakilan jam’iyyar da ta amince su cike sauran gurabu hudu na shugabancin majalisar. Jam’iyyar ta bukaci a ba Sanata Ahmad Lawan shugaban masu rinjaye, sai George Akume mataimakinsa, yayin da ta tura sunan Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Mohammed Monguno kuma mataimakinsa.
Sai dai banagren Saraki ya yi fatali da wannan bukata inda ya bayar da sanarwar nada Sanata Alu Ndume a matsayin shugaban masu rinjaye da Sanata Bala Ibn Na’Allah a matsayin mataimakinsa da Sanata Olusola Adeyeye babban mai tsawatarwa da Sanata Francis Makhana a matsayin mataimakinsa.
bangaren Sanata Lawan sun yi fatali da wannan mataki, lamarin da ya sanya dage zaman majalisar na tsawom wata ba shiri.
A Majalisar Wakilai an daga jijiyar wuya ne inda wasu ’yan majalisar suka ce bai kamata Gbajabiamila ya zama shugaban masu rinjaye ba, saboda mataimakin shugaban majalisar Yusuf Lashun ya fito ne daga shiyya daya da shi. A ranar Laraba wakilan APC da suka fito daga yankin Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Gabas a taron manema labarai daban-daban da suka kira sun zargi shugabannin APC na kasa da yi musu danniya ta hanyar rarraba mukaman ba tare da kebe wa shiyyarsu komai ba.
dan majalisar wakilai na APC daga Jihar Kwara Ahman Pategi wanda ya yi magana a madadin wakilan Arewa ta Tsakiya ya ce sun ji mamaki umarnin jam’iyyar kan rabon mukaman shugabancin majalisar, wanda suke kallo a matsayin tauyewa gare su.
Shi kuma Austin Chukwukere daga Jihar Imo da ya yi magana a madadin wakilan APC daga shiyyar Kudu maso Gabas ya ce “ba za sun ade hannu su bar jam’iyyar ta share ba.” Ya ce, “Bisa tsarin raba-daidai na tarayya, jam’iyyar ba ta yi abin da ya dace ba,” inji shi.