boye Sirri Tsakanin Ma’aurata
Shin ya kamata boye sirri tsakanin ma’aurata? Wannan ya danganta da yanayin dangantakar da ke tsakanin ma’aurata, wasu ma’auratan akwai kyakkyawar dangantaka da aminci a tsakaninsu ta yadda ba sa boye komai ga junansu; a irin haka idan mace ta duba wayar maigidanta bai zama leken asiri ba domin a gabansa ma tana iya yin […]
Shin ya kamata boye sirri tsakanin ma’aurata? Wannan ya danganta da yanayin dangantakar da ke tsakanin ma’aurata, wasu ma’auratan akwai kyakkyawar dangantaka da aminci a tsakaninsu ta yadda ba sa boye komai ga junansu; a irin haka idan mace ta duba wayar maigidanta bai zama leken asiri ba domin a gabansa ma tana iya yin haka. Wasu ma’auratan kuwa komai irin kyawun dangantakarsu ba sa yarda su saki sirrinsu ga juna. Magidanta maza sun fi boye sirrin wayarsu ga matansu; saboda wani sakon ko da ba abin zargi ba ne, wasu matan idan sun gani suna iya mai da shi abin zargi har ya zama sanadiyyar faruwar matsala tsakaninsu da mazansu. Wasu kuma na boye wa ne saboda sun san akwai sakonnin ‘yan matansu da ba su son matan aurensu su gani. Aure wani babban al’amari ne da yake halatta bayyanuwar dukkan sirri ga wanda mutum yake aure; haka kuma shi wani al’amari ne da ke hade mutum biyu su dunkule su zama daya, ba iyakancewa ta zahiri ko badini. Don haka idan akwai kyakkyawar danganta ta kullu tsakanin ma’aurata, ya kamata a ce ba wani boye sirri tsakaninsu. Rashin yarda da amincewa da juna shi yake sa ma’aurata su rika boye sirrin junansu. Kuma shi yake sa su rika zargin juna har ya kai ga dayansu ya rika leken sirrin dayan. Sannan bambanci tsakanin mutane ya sa wasu mutanen suka dauki boye sirri da muhimmanci sosai ta yadda ba sa son kowa ya duba wayarsu ko da kuwa mata ko mijin da suke aure ne, kuma ko da babu wani abin boyewa a ciki.Wasu kuwa ba su damu ba, ko ma waye ya buda ya ga dukkan abin da ya ke ciki ko da kuwa akwai abin zargi a ciki.
Leken Sirri ta Mahangar Addini:
Allah madaukakin Sarki ya hani dukkan Musulmi da yin leken asirin junansu; wannan kuwa ya kunshi har miji da mata. Kamar yadda ya zo a cikin aya ta 12, cikin Suratul Hujrat:
“Ya ku wadanda suka yi imani ku nisanci abu mai yawa na zato; lallai wani sashe na zato laifi ne. kuma kada ku yi leken asirin juna, kuma kada sashen ku ya yi gibar sashe, shin dayanku zai so ya ci naman dan’uwansa matacce? Ba za ku so haka ba, (cin naman, don haka ku ki giba). Kuma ku bi Allah da takawa, lallai Allah mai karbar tuba ne, mai jinkai.”
Don haka mata masu leken asirin waya, da satar makullin wayar mazansu (password) don dai kawai su duba abubuwan da ke ciki su sani wannan babban alkaba’iri ne suke aikatawa domin Allah( S.W.T) Ya yi hani a kan aikata hakan. Ku sani, duk abin da bai shafeka ba, to babu alfanun ka tsunduma kanka a cikinsa; abin nan na rashin dacewa da mazanku suke yi a cikin wayoyinsu; in har ya tabbata da gaske to Ubangijinsu Allah suka saba sama da ku, don haka ba ku da hujjar bincikensu, tuhumarsu ko zarginsu. Da fatan Allah ya ganar da mu duka, ya dora mu a hanya madaidaiciya ta zuwa aljanna, amin.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah ya sa mu kasance cikin kulawarsa a ko da yaushe, amin.