Branyas: Wadda ta fi kowa tsufa a duniya ta rasu a Spain
An haifi Branyas a San Francisco a ranar 4 ga Maris, 1907.
Matar da ta fi kowane mutum tsufa a duniya mai suna Maria Branyas Morera ’yar kasar Spain ta rasu.
Matar wacce aka haifa a Amurka kuma tana raye aka yi Yakin Duniya biyu, ta rasu a makon jiya tana da shekara 117 da kna 168, kamar yadda danginta suka bayyana.
- Tinubu ya kunyata waɗanda suka kyautata masa zato — Sarkin Yaƙin Yarbawa
- Muna yaƙar cin hanci daga tushe — Shugaban EFCC
Kundin Tarihi na Guinness World Records a hukumance ya amince da matsayin Branyas a matsayin wadda ta fi kowa tsufa a duniya a cikin Janairun 2023 bayan rasuwar Bafaranshe Lucile Randon mai shekara 118.
“Maria Branyas ta bar mu. Ta rasu kamar yadda lokaci ya yi; tana cikin barcinta, cikin kwanciyar hankali ba tare da rashin lafiya ba,” danginta suka rubuta a shafinta na X.
“Za mu tuna da ita koyaushe saboda shawararta da kuma alherinta.”
Branyas, wacce ta rayu tsawon shekara 20 da suka gabata a gidan kula da tsofaffi na Santa Maria del Tura da ke garin Olot a yankin Kataloniya a Arewa maso Gabashin kasar, ta yi gargadi a cikin sakon da ta wallafa rana guda kafin rasuwarta cewa tana jin rashin karfin jiki.
“Lokaci ya kusa. Kada ku yi kuka, ba na son hawaye. Kuma dadin dadawa, kada ku sha wahala a kaina. Duk inda na je, zan yi farin ciki,” a cewarta a shafin da danginta ke gudanarwa.
Bayan rasuwar Branyas, mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya shi ne Tomiko Itooka dan kasar Japan, wanda aka haife shi a ranar 23 ga Mayu, 1908 kuma yana da shekara 116 a duniya a yanzu, a cewar Kungiyar Bincike ta Gerontology da ke Amurka.
Branyas, wacce ta rayu a 1918, lokacin da ake Yakin Duniya na Daya da Yakin Duniya na Biyu da Yakin Basasar Spain, ta kamu da cutar Kwarona (COVID19) a shekarar 2020, makonni kadan bayan ta cika shekara 113 amma ta samu murmurewa.
’Yar autarta, Rosa Moret, ta danganta tsawon rayuwar mahaifiyarta da gado.
“Ba ta taba zuwa asibiti ba, ba ta taba samun karayar kashi ba, tana cikin koshin lafiya, ba ta da ciwon komai,” Moret ta shaida wa tashar talabijin na Katalan a shekarar 2023.
An haifi Branyas a San Francisco a ranar 4 ga Maris, 1907 jim kadan bayan danginta sun yi kaura zuwa Amurka daga Meziko.