Brazil: Dilma Rousseff na fuskantar tsigewa

Fiye da kashi biyu cikin uku na ‘yan Majalisar Dattawan kasar Brazil ne suka kada kuri’ar amincewa da gurfanar da tsohuwar Shugabar kasar Dilma Rousseff a gaban kuliya.Ana dai zargin Mis Rousseff da laifin kashe kudin gwamnatin ba bisa ka’ida ba, ba kuma tare da amincewar ‘yan majalisa ba, da daukar bashi a bankunan kasar […]

Brazil: Dilma Rousseff na fuskantar tsigewa
Brazil: Dilma Rousseff na fuskantar tsigewa

Fiye da kashi biyu cikin uku na ‘yan Majalisar Dattawan kasar Brazil ne suka kada kuri’ar amincewa da gurfanar da tsohuwar Shugabar kasar Dilma Rousseff a gaban kuliya.
Ana dai zargin Mis Rousseff da laifin kashe kudin gwamnatin ba bisa ka’ida ba, ba kuma tare da amincewar ‘yan majalisa ba, da daukar bashi a bankunan kasar da nufin cike gibin kasafin kudin Brazil na shekarar 2014.
An dai dakatar da ita daga mukamin ta ne a watan Mayun shekarar, duk da cewa ta musanta zarge-zargen da ake ma ta.
Idan har aka sauke ta daga mukamin shugabar kasa, shugaban rikon kwarya Michel Temer ne zai ci gaba da jagorantar kasar har zuwa lokacin da za a yi zabe a shekarar 2018.
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff, ta gaza shawo kan yunkurin da ake yi na tsigeta daga kan mulki a watan Afrilun bana, bayan wani kwamitin ‘yan majaliasar dokokin kasar ya amince a ci gaba da yunkurin tsigetan.
Kwamitin ‘yan majalisar dokoki mai yawan mutane 65 sun kada kuri’a a watan Afrilun, wadda mutane 38 zuwa 27 suka bayar da shawarar a tsigeta a kan zargin ta yi rufa-rufa a kan alkaluman asusun gwamnatin domin boye gibin da ke cikin asusun.