Brentford ta casa Liverpool a Firimiyar Ingila
Masu tsaron bayan Liverpool sun yi sakaci musamman Konate.
Liverpool ta barar da damar matse hudun farko a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ta sha kashi 3-1 hannun Brentford a filin wasa na Community da ke Landan.
Masu tsaron bayan Liverpool sun yi sakaci musamman Konate, da hakan ya bai wa Brentford damar dawowa mataki na bakwai, maki biyu tsakaninsu da kungiyar ta Anfield.
- Bakin ciki ya sa Obasanjo ke sukar shugabanni — Garba Shehu
- An kai wa Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta kasa hari
Tun a minti na 19 da fara wasa ne Ibrahima Konate ya ci gida bayan an yi bugun kusurwa.
Sai kuma a minti na 42 Wissa ya ci ta biyu aka tafi hutun rabin lokaci 2-0.
To amma jim kadan bayan an dawo a minti na 50 Oxlade-Chamberlin ya mayar da wasan 2-1.
Kuma yayin da Liverpool ta matsa don ganin ta farke ne, dan wasan gaban Brentford Mbeumo ya kwaci kwallo hannun Konate ya ci wa kungiyarsa kwallo ta uku a minti na 84.
A yanzu Brentford ta yi wasa shida ba a doke ta ba, a karon farko da ta yi irin haka a sama da shekaru 80, kuma sun koma na bakwai a teburin Firimiyar Ingila.
Yayin da Liverpool ta barar da damar matse hudun farko da tazarar maki daya, kuma ta cigaba da zama na shida maki biyu kacal tsakaninta da Brentford.