Brice Nguema: Wane ne sabon shugaban mulkin sojin Gabon?
Masu juyin mulkin Gabon sun bukaci kafofin yada labaran Faransa su dawo kasar bayan tsohuwar gwamnati ta kore su
Janar Brice Oligui Nguema shi ne sabon shugaban mulkin sojin kasar Gabon, bayan hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo.
Janar Nguema shi ne Kwamandan Rundunar Tsaron Shugaban kasar, wanda kafin nan ya kasance Babban Dogarin mahaifin tsohon shugaba Ali, wato Omar Bongo, wanda ya rasu a 2009.
- AU ta kira taron gaggawa kan juyin mulkin Gabon
- Juyin mulki: MURIC ta bukaci sojojin Najeriya kada su yi koyi da na Gabon
Nguema wanda mahaifinsa soja na, daya ne daga cikin manyan masu fada-a-ji a Gabon, dan kasuwa ne kuma daya daga cikin manyan attajiran kasar Gabon..
Bayan hawan Ali Bongo kan mulki aka tura Brice Oligui Nguema ya samu horon soji a Kwalejin Horas da Sojoji ta Meknes da ke kasar Morocco.
A shekarar 2019 kuma aka tura Nguema, wanda mahaifinsa soja ne, zuwa kasashen Morocco da Senegal domin gudanar da aikin diflomasiyya.
Shekara 10 bayan zaman Ali Bongo shugaban kasar Gabon aka nada Nguema shugaban rundunar tsaron fadar shugaban kasar, inda ya tsaurara matakan tsaro ga shugaban.
Nguema ya zuba hannayen jari a cikin wani rukunin gidaje a Amurka, inda ya yi ta biyan kudin sannu a hankali, kamar yadda wani bincike da Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Bincike Kan Miyagun Laifuka a Duniya ta gudanar a shekarar 2020 kan kadarorin iyalan Bango suka mallaka a Amurka.
‘Yan jaridar sun kuma gano cewa ya sayi wasu gidaje da kudinsu ya haura Dala miliyan 1 a unguwanni matsakaitan attajirai a Maryland da ke Amurka.
Sun kuma yi masa tambaya game da kadarorin, inda ya ce musu ” wannan batu ne da ya shafi rayuwarsa shi kadai.”
A ranar Laraba, a ranar Laraba, 30 ga Agusta, 2023, sojojin kasar suka nada Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban riko bayan ya jagoranci hambarar da gwamnatin Ali Bongo.
Sojojin Gabon sun dawo da tashoshin labaran Faransa
Sanarwar da suka fitar ta kuma sanya dokar hana fita da dare, kamar yadda gidan talabijin na kasar, Gabon 24 ya sanar.
Sun kuma ba da izini ga kafofin yada labaran Faransa na France 24, RFI da TV5 Monde, wadanda Bongo ya dakatar gabanin zaben kasar.
Kasashen duniya da ma Majalisar Dinkin Duniya sun yi tir da juyin mulkin Gabon, wanda shi ne na tara ke nan a cikin shekaru uku a fadin Nahiar Afirka.
Juyin Mulkin Afirka (2020-2023)
Ga jerin juyin mulki 9 da aka yi a Afirka daga 2020 zuwa yanzu:
- Mali – Agusta 2020: Kanar Assimi Goita ya hamabare Ibrahim Boubacar Keita ya nada Kanar Bah Ndaw.
- Mali – Mayu 2021: Kanar Assimi ya kifar da Kanar Bar ya nada kansa shugaban rikon kwarya.
- Sudan – Oktoba 2021 – Janar Abdel Fattah al-Burhan ya hambarar da gwamnati kan rikicin ’yan siyasa.
- Burkina Faso – Janairu 2022: Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba ja hambarar da Roch Kabore.
- Burkina Faso – Satumba 2022: Kyaftin Ibrahim Traore ya hambarar da Laftanar-Kanar Damiba.
- Chad – Janairu 2021: Mahamat Idriss Deby ya karbi mulki bayan rasuwar mahaifinsa.
- Guinea – Satumban 2021: Kanar Mamady Doumbouya ya hamabrar Alpha Conde.
- Nijar – Yuli 2023: Janar Chiani ya hambarar da Mohamed Bazoum.
- Gabon – Agusta 2023: Har yazu ba a bayyana shugaban sojin ba.
Rainon Faransa
Kusan daukacin kasashen da aka yi juyin mulkin rainon Faransa ne, wadda ke taimaka wa wasu daga cikinsu wajen yakar ta’adanci a yankin Sahel.
Sai dai kuma masu juyin mulki a kasashen yankin na zargin ta da hannu a ayyukan ta’addanci, da kuma mayar da shugabannin farar hula ’yan amshin shatanta.
A kan haka ne gwamnatocin sojin ke korar dakarun Faransa daga kasarsu, inda suke zargin tsohuwar uwar gijiyar kasashen nasu na mulkin mallaka na zamani, da kwashe arzikin kasashensu.
Faransa dai na daga cikin manyan masu neman ganin an dawo da mulkin farar hula a kasahen da aka yi juyin mulkin.
Gabon
An wayi garin Laraba 30 ga watan Agusta da labarin cewa sojojin Gabon sun hambarar da Shugaba Ali Bongo Odimba, sa’o’i kadan, suka soke zaben tare da rufe iyakokin kasar, suka kuma rushe duk masu rike da mukaman siyasa.
Sojojin sun kifar da gwamnatinsa ne sa’o’i kadan ban ya lashe zabe domin fara wa’adinsa na uku a karamar kasar mai arzikin mai da koko da sauransu.
Nijar
Kafin nan a ranar 26 ga watan Yuli Sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki, lamarin da har zuwa yanzu da takwarorinsu an Gabon suka bi sahu ake ake ci gaba da kai ruwa rana wajen ganin sun saki Bazoum, sun mika masa kujerarsa, su koma bariki.
Masu juyin mulkin na Nijar Nijar sun yi tayin mulkin rikon kwarya na shekaru uku kafin su mika wa farar hula, amma kungiyar ECOWAS ta sa kafa ta shure tayin nasu.
Burkina Faso
Kafin Nijar sai da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a Burkina Faso inda a watan Janairun 2022 Laftanar-Kanar Paul-Henri Damiba ja jagoranci kifar da Gwamnatin Roch Kabore kan zargin gaza yakar ta’addancin da ya addabi kasar.
Bayan wata tara a watan Satumba, Kyaftin Ibrahim Traore ya yi masa juyin mulki ya kwace iko da kasar.
Sudan
A ranar 25 ga Octoban 2021, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ja jagoranci sojoji suka kwace gwamnati a juyin mulkin da suka yi bisa zargin rikicin ’yan siyasa da ya jefa kasar cikin rikici.
Guinea
A watan Satumban 2021 Kanar Mamady Doumbouya ya jagoranci sojoji suka yi wa Shugaban Alpha Code na kasar Guinea juyin mulki.
Sojojin sun hambarar da Alpha Conde ne shekara guda bayan ya sauya kundin tsarin mulkin kasar domin ba shi ikon kara wa’adin mulki.
Chadi
A watan Afrilun 2021 sojoji suka ci gaba da mulki a kasar Chadi bayan rasuwa Shugaba Idriss Deby Itno a fagen yaki da ’yan tawaye.
Bayan rasuwarsa ne dansa, Janar Mahamat Idriss Deby ya karbi ragamar shugabancin kasar karkashin mulkin rikon kwarya, wanda wasu ke gani a matsayin juyin mulki a cikin ruwan sanyi.
Mali
Juyin mulki na farko a daga shekarar 2020 shi ne wanda sojojin Mali suka yi a cikin watan Agusta, inda Kanar Assimi Goita ya kifar da da gwamnatin Shugaban Ibrahim Boubacar Keita.
Sai dai maimakon nada kansa a matsayin shugaba, sai ya mika mulkin kasar ga Kanar Bah Ndaw (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya.
Daga baya Kanar Assimi ya kiar da shi a wani sabon juyin mulkin a watan Mayu 2021, ya nada kansa a matsayin sabon shugaban rikon kwarya.